
Yadda aka gudanar da shagalin bikin bude katafaren shagon tufafi na Abubakar Maishadda
Yadda aka gudanar da shagalin bikin bude katafaren shagon tufafi na Abubakar Maishadda
Babban furodusa na masana’antar kannywood Kannywood “Alhaji Abubakar Bashir Maishadda” ya bayyana cewa, daga harkar fim ne ya samo kudin da ya bude katafaren shagon sa na sayar da tufafi da ya kaddamar a ranar Juma’a, don haka ba harka ce da zai yi wasa da ita ba.
Shafin “Fim Magazine” sun ruwairo cewa, ya fada wa mujallar Fim cewa: Harkar fim ita ce ni kaga kuwa in babu ita babu ni, Ko kudin da na bude shago ai da fim na same su fim ba sana’ar da zan bari ba ne.
An yi bikin bude shagon mai suna “Mai Shadda Textile” a ranar Juma’a 30 ga Satumba 2022, wato shago mai lamba 5 dake MYCA 7 Plaza a Titin Gidan Zu jihar a Kano.
A yayin da yake tattaunawa da wakilin mu Maishadda ya bayyana matukar farin ciki yace: Alhamdu lillah babu abin da zan ce wa Allah S.W.T sai dai in gode masa, na kuma yi farinciki sosai da Allah ya nuna mani wannan lokaci.
Kasancewar dama irin wannan sana’ar munayin ta a boye wannan karon sai muka ga ya kamata mu bayyana shi sabida mutane su sani, sabida duk wani abu da ake nema na bangaren yaduddika, shaddodi, jakunkuna, takalma, duk muna da su.
Kuma insha Allahu zamu rika ba da farashi irin yadda ake ba da wa a kasuwa, zai zamana daka shiga cikin kasuwa ka hadu da gosulo ranka ya baci gwanda ka zo wurin mu ka saya.
Dangane da yadda zai iya hada wannan kasuwancin da sana’ar fim kuwa furodusan yace, ai yayar sa da kanwar sa ne zai bar wa aikin gudanar da shagon yayin da shi kuma zai cigaba da harkar sa ta fim.
Yace: Ai wancan kasuwancin ba ni ne a kai ba yaya ta ce da kanwa ta suke kula da shagon.
Harkar fim kuma harka ta ce da nake kan yin ta, harkar fim ita ce ni kaga kuwa in babu ita babu ni, ko kudin da na bude shago ai da fim na same su fim ba sana’ar da zan bari ba ne har gobe ina cigaba da yi.
Mawakin siyasa “Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara” shi ne uban taro a bikin kaddamarwar, wato shi ne ya jagoranci bude shagon.
Dimbin ‘yan fim da suka halarci taron sun hadada Adam A Zango, Daddy Hikima, Nura M Inuwa, Yakubu Muhammad, El-Mu’az Birniwa, Umar Gombe, Rasheeda Adamu Abdullahi, Sadiq Zazzabi, Hafizu Bello, Aisha Ahmad Idris “Aishatulhumaira” da Abba Miko Yakasai, Mustapha Nabraska, Siddiqa J Sarki, da sauran su.
Ita ma matar Maishadda tsohuwar jaruma Hassana Muhammad ta halarci taron tare da ‘yan uwan su na jini.
Tun wajen karfe 3:00 na rana aka fara taron amma ba’a tashi ba sai wajen karfe 10:00 na dare sabida cincirindon mutane.
Rahoto daga👉 Fim Magazine
Ga hotunan a kasa domin ku kalla.