Advertisement
Labaran Hausa

A tarihin kasar Nageriya ba’a taba gwamnatin da talakawa ke shan wahala kamar ta Buhari ba, cewar Sheikh Lawan Abubakar Shu’aibu

A tarihin kasar Nageriya ba'a taba gwamnatin da talakawa ke shan wahala kamar ta Buhari ba, cewar Sheikh Lawan Abubakar Shu'aibu

Fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Kano Sheikh Lawan Abubakar ya caccaki Gwamnatin Buhari yana mai cewa, tun da aka kafa Najeriya talaka bai taba shan wahala kamar a yanzu da Buhari ke mulki ba.

Malam Lawan ya bukaci shugabanni da su ji tsoron Allah su sani talakawa na cikin mummunan yanayi, kuma shugabanni su sani suma talakawa mutane ne kamar yadda shugabanni suke mutane.

Kuma bayin Allah ne kamar yadda kowa yake ba kuma Allah ba ya son su bane da ya bar su ya dauki mulki ya damka wa shugabanni.

A cewar malamin, lokacin Jonathan shinkafa ‘yar Thailand farashin buhunta naira dubu takwas da dari biyar ne, amma a yanzu ta kai dubu talatin da biyar.

Wannan gwamnatin muna fada muna kara nanatawa tare da dukkan girmamawa gwamnati ce data bambanta da sauran gwamnatoci da aka yi a Najeriya, domin duk wani dan siyasa a Najeriya ko dai ya sayi kuri’un talakawa da kudinsa ko yayi cuwa-cuwa ko magudi.

Amma wannan gwamnatin talaka ne ya bata kudi kuma ya zabe ta, amma ba’a taba sanda talaka ke dan dana kudarsa a Najeriya kamar yanzu ba.

Yadda zaka gane lissafin shi ne dauki dukkanin rayuwa a baya zuwa yanzu, nawa ne farashin buhun shinkafa kafin zuwan gwamnatin nan?, nawa ne farashin dala?, nawa farashin manfetur?, daga wanda ya ninka sau hudu sai sau uku.

Dole muyi adalci mu fadi gaskiya mu muka hau kan mumbari muka ce wannan gwamnatin muna kyautata mata zato za tayi adalci.

Don haka dole mu fada mata cewar wannan yanayin da ake ciki bai yi kama da adalci ba, ba wannan ne abun tashin hankalin ba babban tashin hankali shi ne kullum sai an kashe talakawa anyi garkuwa da su.

Sai ace a zo’a yi taron gaggawa na masu ruwa da tsaki, bayan kwana biyu da taron sai a koma gidan jiya, cewar Shaikh Lawan Abubakar.

Ko a kwanakin nan naira tayi mummunar faduwar da ba ta taba yi a tarihi ba wanda hakan ke kara sabbaba wahala da tsadar rayuwa.

An hakkake cewa, matakan Buhari ne na hana ‘yan kasuwa canjin dala da rufe boda suka sabbaba wannan mawuyacin yanayi, tunda jimawa ne dai ake ta kira ga shugaba Buhari da ya cire gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele wanda keda hannu dumu-dumu wajen lalacewar Naira kiraye-kirayen da shugaban yayi watsi da shi.

Mulkin Jonathan kudin kasar Nijar ana samun kowacce jaka a naira 270 amma yanzu sai mutum ya bayar da 1100 za’a ba shi jaka guda.

Farashin dala kuwa ya kai 750 wanda a lokacin Jonathan bata wuce 170-195 lamuran da ‘yan kasa ke kokawa da shi kasancewar Najeriya a yanzu na samun dala wadatacciya duba da yadda farashin gas da fetur ya tashi a kasuwannin duniya.

Kuma da yawan Malaman da zasu iya kawo gyara sun yi shiru da bakinsu sabida sun shiga gwamnatin suna amfana sun gwammace jama’a su sha kowacce irin wahala tun da su suna amfana.

Rahoto daga👉 Hausaloaded

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button