Advertisement
Magunguna

Abubuwan dake hana jin dadin saduwar tsakanin miji da mata da yadda zaku magance su

Abubuwan dake hana jin dadin saduwar tsakanin miji da mata da yadda zaku magance su

Duk da yake anfi ganin cewa mata sunfi maza yawan sha’awa da son jima’i a yanayin halittarsu akan maza, ba abin mamaki bane a sami akasin haka wani lokacin cewa akwai mata da yawa wanda basa da sha’awa ko kwadayin jima’i sabida wasu dalilai na lafiya.

Tana yin kwanciyar aure ne kawai a matsayin wani aiki na biyan bukatar mijinta ba bukatar taba, kuma ba don tana jin dadi ba ko gamsuwa sai dai kawai don bautar aure ko gudun fushin sabawa al’ada, ko kuma domin kare mijinta daga fadawa tarkon zina.

Hakika akwai mata da yawa da suke cikin wannan yanayin rayuwar aure marar dadi wanda sun hakura da hakkinsu na jin dadin aure, inda wasu matan kuma ke kokarin neman mafita daga wannan matsala ta neman hakkinsu daga mazajensu ko neman magani, koma kokarin fahimtar matsalar dake hana su jin dadin da nufin neman warwarar matsalarsu, wannan kalubale ne babba.

Anan zamu ari wasu bayanan lafiya domin bada haske ko bayani akan wasu daga cikin dalilan da yasa wasu mata basa da sha’awa ko basa jin dadin jima’i, ko basa jin dadi sosai ko kuma ma basu taba jin dadin ba a rayuwar aurensu.

Wasu dalilai nada alaka da macen, wasu kuma namijin ne, ga alamomin kamar hama.

(1) Ciwon sanyin mara ko matsalolin mara da mahaifa.

Kama daga sanyin mara (vaginities/toilet infections, UTI & STDs), yoyon fitsari, kululun mahaifa (fibroid), da sauran cututtukan al’aura na daga cikin abubuwan da kan iya hana mace jin dadin jima’i.

Misali, sanyin gaba mai zuwa da ‘yan kananan kuraje a cikin farji na sanya mace taji zafi wajen jima’i yayin da mazakuta ke kai kawo cikin farji, wanda sauda yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen ba cikin al’aura, sai dai suce suna jin zafi lokacin saduwa.

Kurajen suna fashewa sabida gugar da azzakari yake a cikin farji sai wurin ya zama rauni.

Hakan nasa mata tsoron jima’i da ganinsa abin azabtarwa a gare su maimakon abin jin dadi, sau tari basu san abinda ya haddasa zafin ba wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi.

Ciwon sanyi na iya dakushe sha’awar mace ko namiji, ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba (vaginal dryness) wanda alamunsa shine daukewar ni’ima da kaikayin gaba, idan gaba ya bushe zai yi wahala mace da miji suji dadin jima’i in banda zafi.

Haka kuma shima kululun mahaifa (fibroid) yakan ci karo da azzakari cikin farji sai mace taji wani irin yanayi marar dadi lokacin nishadin aure, kuma yana danne mahaifa ya hana haifuwa da kuma sanya yawan zubar jini, don haka neman magani shine mafita.

(2) Budadden Farji

Rashin tsukakken farji yanda zai damki azzakari da kyau domin samar da jin dandanon fata da fata a matse.

Budadden farji kalubale ne dake sanya raguwar jindadi tsakanin ma’aurata, sau da yawa ma’auratan biyu ba zasu sami gamsuwa ba da kyau sa’annan macen baza ta iya jin kololuwar dadi ba, akwai dabarun kwanciya da magani na zamani da zasu iya magance wannan matsala.

(3) Kaciyar Mata wanda ake wuce gona da iri wajan yinta.

kaciyar mata (female circumcision) wacce wanzan ya yanke beli da yawa fiye da yanda ya dace, yin hakan na kashe sha’awar mace idan ta girma, da yawa mata an yanke musu sha’awa a duniya tun lokacinda suna jarirai.

Wasu al’adun a duniya suna yanke beli ne kadan, wasu kuma kamar rabi ne ake fillewa, wasu kuma cire shi suke duka, wato yanke shi suke gaba daya.

Yanke beli da yawa ko duka matsalace dake hana mace jin dadin jima’i, domin kuwa beli (clitoris) shine matattarar jin dadin jima’in mace.

Kamar yanda dai Malamai sukai bayani cewa yin kaciyar mata Mustahabbi ne a Musulunci, Shari’a kuma tayi nuni da cewa kada a wuce gona da iri wurin yankan, ba kamar yanda wasu wanzamai ke aikatawa ba yanzu.

To sai a nemi bayanan Malaman Sunnah domin fahimtar mas’alar baki daya, bugu da kari za’a iya neman magani domin inganta jin dadin aure.

(4) Magunguna.

Ko shakka babu akwai nau’in magungunan turawa ko gargajiya da zasu iya dakushe sha’awar mace, misali magungunan da ake bayarwa domin rage ciwon damuwa ko tsananin bacin zuciyar mutum da sauransu.

Kina mamakin cewa ada kina da sha’awa amma yanzu shiru ne toh mai yiwuwa wannan maganin da kike sha wata da watanni, ko cikin satin nan shine ke sace miki sha’awa.

Yana da kyau duk maganin da aka bawa marar lafiya a asibiti ko wani wuri yasan tutsun maganin wato (side effects nashi) don kada wani abu ya dame shi bai san abinda ya jaza masa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button