Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Abun Mamaki Edwark Mordrake Kenan Da Aka Haifa Da Fuskar Mace A Keyarsa

Abun Mamaki Edwark Mordrake Kenan Da Aka Haifa Da Fuskar Mace A Keyarsa

Abun Mamaki Edwark Mordrake Kenan Da Aka Haifa Da Fuskar Mace A Keyarsa

An haifi Edward Mordrake ne a farkon karni na 19 da wata fuskar ta daban a keyarsa. Sai dai fuskar tasa ta keya bata gani, ko cin abinci ko kuma magana

Amma zai iya amfani da fuskar tasa wurin yin dariya, kuka ko kuma samar da wasu sautuka ba tare da Edward ya iya dakatarwa ba. Sai dai Edward ya bukaci likitoci su cire masa fuskar inda ya koka akan yadda cikin dare yake firgita sakamakon abubuwan da fuskar ke yi.

Ya halaka kansa lokacin yana da shekaru 23 ta hanyar shan guba saboda tsananin tsanar da ya yiwa halittarsa. Yana yawan bayyana yadda fuskar tasa ta keya ke murmushi a lokacin da yake cikin bacin rai, yayin da take kuka a lokacin da yake jindadi.

A lokacin rayuwarsa, a ko wanne dare yana kasa bacci saboda motsin da bakin fuskarsa ta keya ke yi ba tare da wani fitar sauti ba. Fuskar keyarsa ta wata kyakkyawar budurwa ce.

A lokacin rayuwarsa yana kin zuwa ziyara wurin ‘yan uwansa don gudun wani ya firgita ko kuma a tsokane shi.

Masu Sauraranmu A Koda Yaushe Bayan Wannan Labarin Ya Riskeku Zamu So Karben Ra’ayoyinku A Sahen Mu Na Tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button