Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Abun Mamaki Makaho Ya Bayyana Yadda Matarsa Da Kanta Ta Nemi Aurensa

Abun Mamaki Makaho Ya Bayyana Yadda Matarsa Da Kanta Ta Nemi Aurensa

Adeleke ya kara da cewa yana jin dadin zama da matar shi saboda ya yarda da ita sosai kuma yana samun natsuwa a ran shi a duk lokacin da yake tare da ita, kamar yadda majiyar mu ta legit ta wallafa.

Ya kuma ce a lokacin da ta yanke shawarar ta aure shi, mutane da dama sunyi kokarin zuga ta akan kada ta aure shi.

Matar duk bata maida hankali akan masu fada mata kada ta auri shi ba.

Adeleke ya yaba ma matar tashi inda ya bayyana ta a matsayin mace mai ra’ayin kanta, mai kaifin tunani, wacce kuma bayan auren nasu take kokarin yin duk abinda ya shafi walwala da jin dadin shi.

Makahon, wato Ademola Adeleke an haife shi lafiya lau da idanun shi kamar dai sauran mutane.

Sai dai a lokacin da yakai shekara l6 sai wannan matsalar ta makanta ta same shi.

Abinda Ya baiwa mutane da dama mamaki shine yadda yayi kokarin yin karatun zamani duk da wannan hali na malanta da ya tsinci kan shi a ciki, wanda masu idanun ma sai sun yi da gaske, duba da tsarabe-tsaraben dake tattare da hakan.

Makahon wanda dan garin Ibadan ne jihar Oyo ya bayyana cewa bai yi kasa a gwuiwa ba wajen jajircewa don ganin ya cimma muradum shi na yin karatu mai zurfi.

Yayi digirin shi a bangaren aikin jarida, wanda ya ga ma shi cikin nasara.

Da aka tambaye shi ko ta yaya ya rinka yin karatu, makahon ya bayyana cewa ya na zuwa aji ne ya zauna ya saurari farfesoshi.

Sannan ya bayyana cewa an koya mishi yadda ake amfani da injin rubutu da kuma naura mai kwakwalwa, saboda haka ya samu kwarewa.

Ya kara da cewar yana amfani da abun nadar murya wajen daukar darasi, wanda idan ya koma gida yake saurara.

Idan kuma anzo wajen jarabawa, masu tsaron jarabawar a karanto mishi tambayoyin wanda shi kuma yake rubuta wa a cikin na’urar shi.

Ya samu aiki bayan kammala karatu Bayan kammala karatun na shi, makahon ya samu aikin koyarwa da gwamnatin jihar Oyo inda yake dauke
shi malamin koyar da nahawun turanci.

Yace yana samun dogaye daga cikin daliban shi da suke mishi rubutu a kan allo a yayin da yake gudanar da darasi.

cikin daliban shi da suke mishi rubutu a kan allo a yayin da yake gudanar da darasi.

Ya yaba ma kyakkyawar matar tashi sosai bisa yadda take fara gabatar da bukatun shi kafin nata, ya kuma kara da cewa matar tashi abin dogaron shi ce.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button