
Abun Mamaki Yadda Wata Mata Yar Shekaru 60 Ta Haihu ‘Ya’ya A Rana Daya
Abun Mamaki Yadda Wata Mata Yar Shekaru 60 Ta Haihu 'Ya'ya A Rana Daya
Bayan tsawon shekaru da dama tana jiran tsammani, Allah ya albarkaci wata yar Najeriya mai suna Chinwe Mbahotu da haihuwar yan uku.
Mbahotu, wacce shekarunta suka haura 60 a duniya ta haifi maza biyu da mace daya.
Wani dan uwan matar, Cliff Ayozie, ne ya wallafa labarin mai dadi a shafin Facebook, inda ya bayyana cewa ta haihu ne a Dallas, kasar Amurka a cikin makon jiya.
Ya rubuta a shafin nasa:
“Uwa a shekaru 60t Allah ya albarkace ta da samun yan uku. Maza biyu da mace daya a Dallas, US. Uwa da ya’ya na cikin koshin lafiya. Yar uwata, Chinwe Mbahotu na ta tsammanin wannan kyauta na musamman a tsawon shekarun aurenta. Yanzu, Ubangiji ya ziyarceta don sauya shekarun bakin ciki zuwa na farin ciki da murna. Ku taya mu addu’a da farin ciki.”
Jama’a sun yi mata fatan alkhairi
Bernard Ejiogu ya yi martani
Allah da girma yake. Ina taya ki murna kuma Alah ya baiwa uwa da yayan lafiya.”
Evelyn Ekpen-Nwosu ta ce:
“Ubangijinmu kenan. Shekara dubu kamar kwana daya ne a wajensa.”
Okwuonu Victor ya ce:
“Wow.wannan labara ne mai dadi. Allah mun gode maka!”
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.