Labaran Hausa
Trending

Abun Rabo Ne Yadda Wata Dalibar Jami’a Ta Samu Karywar Ta Haihu ‘Ya’Ya Biyar A Lokaci Guda

Abun Rabo Ne Yadda Wata Dalibar Jami'a Ta Samu Karywar Ta Haihu 'Ya'Ya Biyar A Lokaci Guda

Oluomachi Nwoye, dalibar ajin karshe a jami’ar ilimin noma ta Michael Okpara ta samu karuwar jarirai biyar a rana daya a asibitin tarayya na Umuahia a jihar Abia.

Mahaifiyar Oluomachi ta ce jariran biyar da diyarta ta haifa sun hada da maza biyu da mata uku, kuma ta haihu ne da misalin karfe 9:15 na dare.

A wani rahoton Vanguard, an ce biyu daga jariran kuma maza na karbar kulawa ta musamman kasancewar an haife su da ‘yar matsala.

Mahaifiyar tata, Mrs Priscilla Nwojo ta ce ta shiga farin ciki da samun wannan kyauta daga Allah.

Sai dai, tace irin wannan baiwa da Allah ke bayarwa na iya zuwa da matsalolin da ba a rasa ba.

Daga nan ne ta nemi gwamnati ta kawo musu tallafi domin samun damar kulawa da wadannan jarirai da suka samu.

Hakazalika, ta ce suna neman taimako daga mutanen da za su iya, inda ta ba lamar waya kamar haka 08035746487 tace a kira domin neman kari bayani

Saide mutane sunyi martanin kan wannan Lamarin

Christian Grace Nmesomachi tace: “Ina tayaki murna ‘yar uwa. Babu abin da Allah ba zai iya yi ba…Allah zai baki duk abin da kike bukata na kula dasu har girma.

Marvellous Atuliwa yace: “Ina taya uwa da dangin nan murna.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button