Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Abunda Ya Faru A Shari’ar Dan China Da Ya Kashe Budurwa Yar Nijeriya Wato Ummita

Abunda Ya Faru A Shari'ar Dan China Da Ya Kashe Budurwa Yar Nijeriya Wato Ummita

Kamar yadda kuka Sani A Cikin Watan Da Ya Gabata Ne Aka Samu Wani Mummunan Al’amari Da Ya Bawa Mutane Mamaki Ta Yadda Wani Dan China Yazo Har Nijeriya Tare Da Kashe Budurwarta Ummita

Inda Bada Jimawa Da Yin Wannan Aika Aikar Ba Sai Yan Sanda Sukayi Nasarar Chafke Shi Inda Wasu Daga Yan China Sukayi Allah Wadan Wannan Sayen Aikin Da Yayi

Saide An Fara Gudanar Da Shari’ar Ne Sai Aka Dage Shari’ar Inda A Yau 3 Ga Watan Satumbar 2022 Aka Cigaba Da Shari’a

Inda Daga Bisani Kuma Gidan Jarida Bbc Hausa Suka Bayyana Cewar ‘An dage shari’ar dan Chanar da ya kashe Ummita a Kano.

An dage zaman kotun zuwa 27th ga watan Oktoba har sai an samarwa da Mr. Geng Quangrong, wanda zai yi masa tafinta daga turanci zuwa Chanisanci.

Ba a jima da fara zaman kotun ba ne aka dage zaman saboda matsalar rashin fahimtar bayanai daga bangaren Mista Geng, wanda ake zargi da kisan Ummukulsum Sani Buhari, da aka fi sani da Ummita, a Kano’

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button