
Ahmad Bifa Amaryar Tiktok yayi martani kan cewa matar aure ce bada sanin iyayenta ta shiga harkar fim ba
Ahmad Bifa Amaryar Tiktok yayi martani kan cewa matar aure ce bada sanin iyayenta ta shiga harkar fim ba
Karon farKo Amaryar Tiktok tayi martani dangane da rigimar da akeyi akanta kan cewa, shin da gaske tana da aure take Fim ko kuma Mijinta ya saketa kafin ta shiga harkar Fim din Hausa.
Hakan yasa aketa cece-kuce tare da kara budewa ‘yan Fim din Hausa wuta, musanman ma mai shirya shirin na Amaryar Tiktok, wato Ahmad A. Bifa.
Hakan yasa a nemi jin gaskiyar lamarin inda an tuntubi mashiryin shirin na Amaryar Tiktok kan shin da saninsa yasa Matar aure a cikin shirinsa.
Inda shi kuma ya bada amsa da cewa: ba shi ya kawota harkar fim ba, dama tun kafin fim din sa na Amaryar Tiktok tayi fina-finai da dama, sannan kuma ta tabbatar masa da cewa bata da aure sun rabu da Mijinta har ma ta fara biyan Mijin nata kudaden sakin data nema yayi mata.
Shi kuma a bangaren Mijin nata cewa yayi, duk wannan zancen na Ahmad Bifa daya fadi duk zance ne na kanzon kurege, domin ba gaskiya bane.
Ga cikekkiyar bidiyon a kasa domin ku kalla.