Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Akan Rarara Zan Iya Cin Uwar Kowa Kuma Ni Babban Lakcara Ne Ba Maula Nake Ba

Akan Rarara Zan Iya Cin Uwar Kowa Kuma Ni Babban Lakcara Ne Ba Maula Nake Ba

Tsohon jarumin Kannywood, Aminu Ahalan ya bayyana a wani bidiyo da ya saki a shafinsa na TikTok inda ya dinga surutai yana zage-zage game da masu sukarsa akan yabon mawaki Rarara da hawa wakarsa da yake yi, Bakori Celebrites na Facebook ya ruwaito.

Ya fara da cewa:

“Salam, wannan bidiyon naku ne, musamman marasa kunyar nan na TikTok. Abinda nake so in gaya muku ba. Duk cikinku babu wnada ya isa, gajojin banza da na wofi.“

A cewarsa, ya kula da ‘yan bani na iya da kuma Wawayen da ke kafafen sada zumunta da su ke caccakarsa da zarar ya yabi Rarara, kuma a ya ce ba ya neman komai a wurin mawakin.

A cewarsa Rarara yana kokari kwarai wurin kyautata wa jama’a kuma shi din ba jahili bane, don lakcara ne a jami’a. Ya ja kunnen jama’a inda yace shi da babban mutum ne, kada aga yana harka a soshiyal midiya tare da jama’a amma shi din ba karamin mutum bane.

Ya yi zagi masu nauyi ga duk masa sukarsa inda yace ya wuce da saninsu, kuma su kiyaye shi tunda su jahilai ne marasa kunya da mutunci.

“Akan mawaki Rarara zan ci uwar kowa, banzaye, jahilai, Ass holes. Tunda ba ku da hankali, bari nima in yi alfahari. Ni lakcara ne, na fi karfinku. Kuma Rarara ya fi karfinki.

“Ban yi wa ministoci, ko sanatoci roko bane zan yi wa Rarara? Ni dai kawai ina son shi ne. Kuma ayyukan da yake yi su na burge ni. Don haka ku jahilai ne. Kuma ba ta taku nake yi ba.”

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Source :Labaran Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button