
Alamonin da Namiji zai gane yana da raunin mazakuta, da yadda zaku karawa gabanku karfi da kuzari
Alamonin da Namiji zai gane yana da raunin mazakuta, da yadda zaku karawa gabanku karfi da kuzari
Wadanne alamomi ne mutum zai ji ya fara tunanin yana da matsalar raunin mazakuta?.
1. Rashin Mikewar Azzakari: Haka na faruwako da an yi tunanin jima’i ko kuma ma ansamu haduwar jikin mace da shi maimatsalar.
2. Saurin Kwantawar Azzakari: Abin nufi a nan shine azzakarin zai mike sai dai ba da jimawa ba sai ya kwanta, tun kafin aje ga saduwa ko kuma da zarar an fara.
A lura wannan na da banbanci da saurin kawowa, saboda a nan zata kwanta ne ba tare da mai matsalar ya kawo ba.
3. Rashin Sha’awa: Mai wannan matsala zaiji ba ya sha’awar saduwa da iyali, ma’ana gaba daya sha’awarsa ta gushe.
Kamar yadda mu ka ambata tun da farko duk mai fama da daya ko wasu daga matsalolin can da mu ka zana a sama, magance su shine warakarsa da ikon Allah.
Duk da haka Hausawa kan ce, idan kana da kyau ka kara da wanka bayan magance kalubalen lafiya da ake fama da isu, za’a iya amfani da wadannan hade-hade da zamu zana a kasa.
Hakanan, ko da mutum ba ya fama da daya daga cikin wadancan matsaloli, masana na bada shawarar yawaita motsa jiki da kuma lurada nau’in abincin da ake ci.
Hakika Allah Madaukakin sarki ya halicci gangar jikin mu daban-daban, sakamakon haka yasa, maganin karin kuzarin namiji da sauran magunguna sukan bambanta ne daga wani mutumin zuwa wani.
Ba lallai ne maganin da wani ya sha yayi masa aiki kuma wani mutum ya sha ya dace ba, wannan dalilin yasa muka ga dacewar kawo nau’i daban-daban idan ka gwada ba ka dace ba zaka iya dacewa a wani.
1. Dabino: Yadda ake amfani da shi shine, ka samu dabinonka mai kyau guda 13 ko15 sai ka wanke ka zuba a mazubi mai tsafta, sai ka zuba ruwa ya sha kansa kabar shi tsawon awa uku sannan ka cinye, idan da hali ayi safe da yamma, amma idan ba hali sai aci da yamma kadai.
Sai dai ba’a son aci wannan hadi da zarar an kammala cin abinci idan son samu ne ana son aci lokacin da ake jin yunwa, sai ajira mintuna 20 zuwa 30 kafin aci wani abinci.
2. Kwai: za’a samu kwan kaza guda 2 babban cokali 1 na garin habbatus sauda, sai a cakuda su sosai sannan a soya sama-sama kar ya kone, sannan a cinye.
3.KANKANA: Kankana na kunshe da wasu sinadarai dake aiki kwatankwacin maganin karfin maza na zamani da ake kira Viagra’ a turarnce, don haka tanakara karfin maza sosai.
Don a samu amfaninta sosai za’a sha mintuna 30 kafin fara jimai, ana bukatar a cinye har wannan farar tsokar da kuma ‘yayan wannan farar tsokar da kuma ‘yayan.
kuma kar a sha lokacin ciki na cike, amfi son a sha kafin cin abinci kuma a saurara bayan an sha zuwa mintuna 20 zuwa 30 kafin abi ta da abinci.
4. Ayaba: Tana da sanadarai dake karawa namiji kuzari sai aci guda uku ko biyu kafin jima’i da mintuna 30, kamar kankana ba’a son cin ta da zarar an kammala cin abinci.
5. Man Kanumfari: shi kuma za’a samu mai kyau wanda ba shi da hadi sai a shafe azzakari gaba daya mintuna 30 kafin jima’i.
6. Namijin Goro: Cin namijin goro a kalla guda biyu a rana ya kan dawowa da namiji kuzarinsa, an jarraba an tabbatar da hakan sakamakon wasu sanadarai dake cikinsa mai matukar fa’ida wajen samar da karsashi ga maza.
Fadakarwa: Akwai bukatar mu kauracewa amfani da maganin karin karfin maza na nasara ba tare da shawarar likita ba, saboda illolinsu ga lafiya.
Allah yasa mudace.