
Labaran Hausa
Allah ya azurta Daraktan fina-finan hausa Saifullahi Safzor da santaleliyar ‘yar mace
Allah ya azurta Daraktan fina-finan hausa Saifullahi Safzor da santaleliyar 'yar mace
Allah ya azurta daraktan fina-finai masana’antar kannywood “Malam Saifullah Isyaku ldris” wanda aka fi sani da Safzor da santaleliyar ‘yar mace.
Matar sa mai suna “Khadija” ta haihu a ranar Asabar 1 ga watan Oktoba 2022, da misalin karfe 11:30 na dare a wani asibiti mai suna Al-Munir dake kusa da unguwar NDA a Kaduna, kamar yadda “Fim Magazine” suka ruwaito.
Kamar yadda a yanzu ba a jira sai ranar suna ake bayyana sunan jariri suma sun rada wa ‘yar tasu suna Amina, amma suna kiran ta da Minal.
A ranar mai zuwa za’a yi taron suna in Allah yakai mu, Allah ya raya Amal bisa tafarkin Manzo tsira “S.A.W” ya albarkaci rayuwar ta ameen.