Advertisement
Labaran Hausa

Allah ya sanya da alkairi: Mawaki Umar M Shareef zai angwance da nan gaba kadan

Allah ya sanya da alkairi: Mawaki Umar M Shareef zai angwance da nan gaba kadan

Fitaccen mawakin kannywood wato “Umar M Shareef” ana tunanin zai kara aure inda yanzu haka gari ya rikice da ganin wasu zafafan hotunan bikin nasu shi da Amaryarsa wanda mutane suke taya shi murna da kuma farin ciki akan wannan al’amari.

Domin wannan mawakin yana bayar da gudun mawa mai karfi akan sha’anin duk wani biki ta hanyar yin waka.

Sai gashi shima yanzu nasa yaso kunga dole a rama masa biki domin yadda ya kasance ba shi da kiwa da ance lamarin biki zaka same shi akwai shida hanzari kuma yakan sanya Ango da Amarya a cikin farin ciki wanda haka ake fata a lokacin biki.

Babban abinda mutane basu sani ba shine idan harta tabbata wannan mawakin auren zaiyi da gaske to jama’a su sani cewa, bawai shine auren sa na farko ba wanda a kalla wannan mawakin ya haura shekara goma da matarsa.

Wannan ba karamin abin alfahari bane mutum yayi aure yana da kuruciyar sa.

Tashar “Amo Hausa Tv” dake kan manhajar Youtube sun wallafa labarin auren mawakin tare da wacce zai aura.

Ga bidoyon nan a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button