Advertisement
Labaran Hausa

Allah ya yiwa Shehu Lili sabon Ango rasuwa jim kadan bayan daura auren sa

Allah ya yiwa Shehu Lili sabon Ango rasuwa jim kadan bayan daura auren sa

Wani matashin ango mai suna Shehu Lili Kofar Atiku ya rigamu gidan gaskiya sa’o’i ashirin da hudu bayan an daura masa aure a jihar Sokoto, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruqaito.

Wani abokin angon “mai suna Shamsudeen Buratai” shine ya tabbatar da aukuwar lamarin, Buratai ya bayyana cewa Shehu Lili ya rasu bayan yayi fama da ‘yar gajeruwar rashin lafiya.

A cewar Buratai, an daura auren angon ne a ranar Lahadi 5 ga watan Oktoba 2022, da misalin karfe biyar na yammna a unguwar Kofar Atiku, sannan ya rasu da safiyar ranar Litinin.

Shehu abokina ne tun na yarinta kuma dan’uwa na tsawon fiye da shekara 30,  yana fama da matsananciyar malaria wacce take taso masa duk lokacin sanyi.

Kamar kowace shekara, Ciwon nasa ya taso masa a bana a cikin watan Disamba, inda ya sha magunguna ya samu
lafiya, a cewar sa.

Da safiyar yau misalin karfe tara na safe, ya fito inda muka gaisa yadda muka saba, kwatsam kawai sai ya fara jin wani bakon yanayi inda yace mana yana tunanin ciwon malaria ne yake kokarin dawo masa.

Kafin mu yi aune kawai har ya fadi kasa, shikenan karshen sa kenan, kamar yadda Shamsu ya bayyana.

Tuni dai har an binne mamacin bisa yadda shari’ar musulunci ta tanada, muna addu’ar Allah (SWT) ya jikansa da rahama ya gatarta masa yasa aljannah ta zama makoma a gare shi, mu kuma idan tamu tazo yasa muyi kyakkyawan karshe na cikawa da imani.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button