Labaran Hausa
Trending

Amarya Ta Fada Tahin Hankali Bayan Ana Tsaka Da Bikinsu Yan Bindiga Suka Harbe Angonta

Amarya Ta Fada Tahin Hankali Bayan Ana Tsaka Da Bikinsu Yan Bindiga Suka Harbe Angonta

An harbe wani ango har lahira a yayin da ake tsaka da shagalin bikinsa a cikin kuskure inda aka bar wa amarya gawarsa kwance cikin jini.

Marco Antonio mai shekaru 32 yana rike da hannun matarsa yayin da yake tattaki zuwa mota bayan an daura aurensu a coci yayin da aka bindige shi a Caborca ake Mexico.

An sakankance cewa an harbi injiniyan ne a bisa kuskure kuma an yi nufin harbin wasu gungun jamaa ne dake safarar kwayoyi a birnin.

An ga hoton matarsa cike da tashin hankali a cikin jini bayan wanke mata riga da yayin yayin da take taimakon masoyinta.

Yar uwar Antonio ma an harbeta a bayan kamar yadda jaridun yankin suka tabbatar.

Jami’ai sun tabbatar da cewa Antonio ya sheka lahira bayan farmakin da aka kai masa da bindiga wanda ake gani a matsayin kuskure.

Carboca madaddala ce ta fitacciyar kungiyar masu safarar kwayoyi ta Caborca wacce fitaccen mai safarar kwayoyi Rafael Caro Quintero ke shugabanta. Kungiyar a halin yanzu
tana dauki ba dadi da Los Salazar kan safarar kwayoyi.

Jami’i mai binciken lamarin yace “Bincike ya nuna cewa harin da ya samu Marco Antonio an yi nufin samu wani ne wanda ke aure a wannan ranar amma a birni mai kusanci da nan.

kuma duk wasu rahoton kwararru ana cigaba da karba domin samun gamsassun bayanai tare da aiwatar da abinda ya dace kan wadanda suka yi laifin.”

Hakazalika, kamar yadda LIB suka rahoto, an harbe wani ango a birni mafi kusa duk a wannan daren.

Gwamnan jihar, Alfonso Durazo yace

“Wannan farmakin an aiwatar da shi ne saboda mutum daya kuma hakan na nufin ba da kowa zai faru ba.”

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button