Advertisement
Labaran Hausa

Amfani Da Magunguna 5 Da Gwanda Keyi A Jikin Dan Adam Da Ya Kamata Ku Sani

Amfani Da Magunguna 5 Da Gwanda Keyi A Jikin Dan Adam Da Ya Kamata Ku Sani

Gudumawar da gwanda ke bai wa lafiyar jikin dan Adam na da tarin yawa. Tana dauke da sinadaran magani sanannu da jama’a da yawa a fadin duniya suka sani.

llimi ya nuna cewa gwanda tana dauke da sinadaran Vitamin A, C, E da K.

Tana kunshe da Magnesium, potassium, niacin, carotene, protein, fiber da kuma papain, wanda ke maganin mura da kashe wasu kwayoyin cuta a jiki.

Za ka sha matukar mamaki idan ka gano amfanin gwanda.

Abin mamakin shine, bincike ya nuna cewa hatta ya’yanta na matukar ta imakawa fatar dan Adam tare da sanyata walkiya.

Ga wasu amfanin gwanda 5 ga dan Adam.

1. Tana kara hasken fata Sanannen abu ne cewa gwanda tana goge fata tare da taimakawa wurin cire dattinta. Kunsar sinadarin Vitamin C da tayi yasa take bada kariya wurin lalacewar fata.

2. Tana hana bayyanar alamun tsufa ko shekaru Gwanda tana saka fata ta yi laushi da santsi Tana iya bada wannan amfanin ne sakamakon sinadaran Vitamin da ke cikinta.

Akwai sinadarin alpha hydroxy acid wanda ke hana bayyanar alamun shekaru ta hanyar kashe matattun ya’yan halitta. Vitamin C da E suna
boye shekaru tare da rage tsufa.

3. Tana yakar fimfus da tabbansu

Bincike ya nuna cewa sinadarin Papain da ke kunshe a gwanda na goge fata. Hakan yasa kofofin fata da suke toshe ke budewa.

Hakazalika, matacciyar fata na fita da taimakon sinadarin hydroxy acid. Hakan na hana fimfus da tabbai.

4. Gwanda tana hana bushewar fata

A nan, ‘ya’yan gwanda na bada mamaki. Ana amfani da su ga fata mai laushi ko mai tauri.

Sakamakon sinadaran Vitamin da Minerals da ta kunsa, tana hana bushewar fatar mai amfani da ita

5. Gwanda na maganin tattarewar fata
sakamakon tsufa da kuma tsagewar kafa yayin sanyi

Bincike ya nuna cewa gwanda na hana bayyanar tattarewar fata sakamakon tsufa sannan tana maganin tsagewar kafa yayin sanyi.

Tun a farko an san tana kunshe da sinadaran Vitamin G, wannan kadai yana iya yakar duk wani abu da ke lalata fata.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button