
Amfanin Man Zaitun A Jikin Dan Adam Har Kara Karfin Mazakuta Yanayi
Amfanin Man Zaitun A Jikin Dan Adam Har Kara Karfin Mazakuta Yanayi
KARFIN MAZAKUTA
Duk mutumin da ya samu kanshi a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa acikin ruwan danyan kwai sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum.
insha Allah zai samu karfin mazakuta sosai Kada ka gaji duk wani magani da kagani ka gwada zaka dace insha Allah
CIWON CIKI
Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatussauda ya cakuda ya sha safe da yamma.
CIWON KAI
Duk mutumin da yake ciwon Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali daya da safe da Rana da dare insha Allah zai samu lafiya.
CIWON HAKORI
duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganya zaitun da ya’yan habbatussauda ya sakasu acikin garwashi ya buda bakinsa hayakin ya dinga shiga, insha Allah.
CiwON HANTA
duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali daya da safe daya da Rana daya da dare.
CIWON SUKARI
duk mutumin da ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci insha Allah
Ciwon Asma
duk mutumin da wannan ciwon ya kamashi,to sai ya samu ganyen zaitun ko ya’yan sa ya dinga turara wa.
ClWON KODA
duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a Rana insha Allah.
CIWON RAMA
duk mutumin da yaga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku insha Allah zaiyi kiba.
ZAZZABI MAI ZAFI1
duk mutumin daya kamu da zazzabi mai zafi to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya sannan yana karanta ayatul kursiyyu sau 7 yana tofawa acikin yana shafe jikinsa dashi insha Allah.
ZUBEWAR GASHI.
duk mutumin da gashinta baya futowa sosai ko in ya futo sai ya zube, to saita samu ruwan zafi ta wanne kanta dashi sannan bayan ya dan bushe saita zuba man zaitun a hannun ta, sai ta shafe kannata dashi gaba daya kullum.
KARANCIN JINI
duk mutumin da yake da karanci jini a jikinsa to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu Rana.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.