Advertisement
Labaran Hausa

An ɗaura: Jarumin Kannywood Yusuf Saseen ya zama angon Amina

An ɗaura: Jarumin Kannywood Yusuf Saseen ya zama angon Amina

ƘARSHEN tika-tika, tik! Jarumin Kannywood Yusuf Muhammad Abdullahi (Saseen) ya zama ango.

A yau Asabar, 24 ga Disamba, 2022 aka ɗaura auren sa da masoyiyar sa Amina Zakari Yunusa Daya.

An ɗaura auren da misalin ƙarfe 11:00 na safe a gidan Makaman Fika da ke layin makaranta a garin Potiskum cikin Jihar Yobe, a kan sadaki N50,000.

Bayan ɗaurin auren an yi walima.

Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci ɗaurin auren su ne Ahmad Bello (Naziru a ‘Daɗin Kowa’),  Aminu Saira, Umar UK, Ibrahim Birniwa, Isah Ferozkhan, Aminu Unguwar Gini, Yasin Auwal, Sani Mai Iyali, Murtala Sani da Ahmad Nagudu.

Yau kuma in Allah ya kai mu lafiya za a yi dina a Kano.

Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button