
An kama wani magidanci bayan ya cinnawa matar sa da ‘yayan sa wuta sabida taki amincewa suyi kwanciyar aure
An kama wani magidanci bayan ya cinnawa matar sa da 'yayan sa wuta sabida taki amincewa suyi kwanciyar aure
Wani magidanci ya cinnawa ‘yayan matar sa guda biyar wuta bayan ta hana shi suyi kwanciyar aure.
Magidancin mai suna “Ojo Joseph” mai shekara 54 a duniya ya aikata wannan aika-aikar ne a jihar Ondo, lamarin ya auku ne a unguwar Fagun cikin garin Ondo a ranar Lahadi 6 ga watan Oktoban 2022 dasafe, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
Joseph ya fusata ne inda ya cinnawa yaran wuta bayan mahaifiyar su taki yarda suyi kwanciyar aure.
Wanda ake zargin ya watsa manfetur a dakin da yaran ke yin barci sannan ya cinna masa wuta.
Daya daga cikin yaran ya kone har lahira yayin da sauran suka samu munanan raunika inda ake duba lafiyar su a babban asibitin tarayya dake Owo.
Matar sa da tagwayen da suka haifa tare masu watanni sha takwas aduniya sun tsira daga wutar da ‘yan kananan raunika.
Da take tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar “Funmi Odunlami” ta bayyana cewa, tuni aka kama magidancin.
Ta kuma kara da cewa, an fara gudanar da bincike sannan za’a kammala kafin a tura wanda ake zargin zuwa kotu bisa zargin sa wuta da kisan kai.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa