
Ana wata ga wata: Jarumar Kannywood Maryam Booth na shirin komawa kungiyar su Mr442 da Safara’u
Ana wata ga wata: Jarumar Kannywood Maryam Booth na shirin komawa kungiyar su Mr442 da Safara'u
Yau kuma jirgin 442 ya haura kan jaruma Maryam Booth inda itama ta shiga cikin su sabida ta kara suna banda abinta kuma ai wannan ba shine zai sa tayi suna ba, domin irin suna da tayi wayannan mawakan ko kamo kafar ta basuyi ba amma kuma wai a haka ta koma jikin su domin ta kara suna a idon duniya.
An ganta a jikin su suna bidiyo tare kuma wannan abin ya bawa mutane mamaki musamman ‘yan uwanta jarumai na kannywood, domin yadda suke kallo wannan jarumar a matsayin mace me kamun kai amma kuma zata bata rawarta da tsalle wannan ta bawa mutane kunya.
Sai dai kuma masoyanta suna ta yabon wannan abinda tayi inda suke kareta suke cewa sam jarumar bazata taba komawa wajen wannan mutanen ba kasancewar sun yadda da ita domin sun san bazata taba komawa wajen suba.
Ga cikekkiyar bidiyon a kasa domin ku kalla.