Labaran Hausa

Ana zargin jarumin kannywood Baba Ari da lagadawa malamar islamiyya duka sabida ta daki ‘yar sa

Ana zargin jarumin kannywood Baba Ari da lagadawa malamar islamiyya duka sabida ta daki 'yar sa

Wata Malamar makarantar Islamiyya a anguwar Mubi kusa da Kofar Nasarawa a cikin birnin Kano, ta zargi jarumin fina-finan Kannywood na barkwanci Aminu Baba Ari da lakada mata dukan tsiya.

A cewar ta, bai bar ta ba har sai da ta fadi kasa tare da yunkurin taka ta da takalmin sa, Malama Zainab ta bayyanawa Mujallar Fim yadda lamarin yafaru inda tace a cikin yaran da take koyarwa akwai diyar Baba Ari.

Tace, sun aikata laifin da suka cancanci hukunci ne ita kuma ta hukunta su, sai dai da tazo kan yarinyar ta rike bulalar tare da kafewa cewa Lallai ba za’a duketa ba.

A yunkurin dukan nata ne ta fadi kasa, inda aka ce Aljanununta sun tashi, Malama Zainab ta cigaba da bayyana cewa:

Bayan Baba Arin ya samu labarin yadda lamarin ya auku ne yazo har Islamiyyar ya rufe ni da duka har na kai ga faduwa kasa, anan ne yayi barazanar taka ni da takalminsa.

Bayan aukuwar wannan lamarin ne shugabannin makarantar suka nuna rashin jin dadin, su sannan suka lashi takobin daukar mataki akan cin zarafin da aka yi wa malama Zainab don gudun kara faruwar hakan.

Yayin da Mujallar Fim ta tuntube shi Aminu Baba Ari yace, shi bai daki Malamar ba, ya dai daki dankwalinta ta baya ne.

Ya cigaba da cewa: A yanzu dai mun dai-dai ta kuma komai ya wuce.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button