Advertisement
Labaran Hausa

Auren Adamsy Celebraty Da Uammakatty Sun Zama Tif Da Taya

Auren Adamsy Celebraty Da Uammakatty Sun Zama Tif Da Taya

JARUMI a Kannywood, Adam A. Adam, wanda aka fi sani da Adamsy Celebrity, ya yi bankwana da kwanan shago.

A ranar Asabar, 10 ga Disamba, 2022 aka ɗaura auren sa da sahibar sa, Ummu-Khursum Muhammad Tamula (Ummakatty).

An ɗaura auren ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a masallacin Zawiyya da ke Zololo, Jos, Jihar Filato, a kan sadaki N350,000

Kafin ranar ɗaurin auren, an gudanar da shagulgulan biki irin su ‘cocktail party’, ƙwallon ƙafa, dina da Ranar ‘Yan Wasa.

‘Yan fim da mawaƙa da su ka halarci bikin sun haɗa da Ado Gwanja, Hamisu Breaker, Kawu Ɗansarki, Ɗanmusa, Al-Amin Buhari, Abubakar S. Shehu, Ahmad Delta, KB International, Tynking Mai Gashi, Yamu Baba, Gombe, Ahmad Shanawa, Aminu S. Bono, Umar Big Show, Yunusa Mu’azu, Abba Sadau, Bello Muhammad Bello, Z Square, Geena, Bilkisu Abdullahi, Maryam Yola, Ummi Ƙarama, Zainab Ishola, A’isha Channel 7, Murja Ibrahim Kunya da Zainab Sambisa.

Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button