Labaran Hausa

Auren da Maryam A.B Yola tayi na cin amana ne, cewar kawarta Sapna Aliyu Maru

Auren da Maryam A.B Yola tayi na cin amana ne, cewar kawarta Sapna Aliyu Maru

Jarumar KannywoodSapna Aliyu Maru ta bayyana cewa, auren da kawar ta Maryam A.B Yola ta yi jiya na cin amana ne, domin kuwa saurayin ta ne ta aure, kamar yadda “Fim Magazine” suka ruwaito.

Sapna ta fada wa da mujallar Fim haka ne bayan an daura auren Maryam din da wani matashi mai suna Muhammad Murtala.

A ranar Juma’a 30 ga watan Satumba, 2022 aka daura auren tsohuwar matar Adam A Zango Maryam A.B Yola tare da Muhammad, wanda dan kasuwane kuma dan jarida wanda dan asalin jihar Borno ne da yake gudanar da kasuwancin sa a tsakanin Legas da Fatakwal.

Amaryar, wadda ita ma sananniyar jaruma ce a masana’antar Kannywood ta wallafa bidiyo biyu a shafin instagram ita kadai ta na rawar murna cikin shigar amarci.

A dayan bidiyon kuma ita da angon ta suna yiwa juna kallon kuda, abokan arziki da dama sun taya murnar wannan abin farin ciki da ya same ta.

Amma dai ita Sapna tace lallai Maryam ta ci amanar ta domin ita da Muhammad sun dade da shirya maganar yin aure.

Tayi mamakin yadda duk da kusancin ta da Maryam amma taci amanar ta ta aure mata masoyi, sai dai ba tayi cikakken bayani ba kan wannan ikirarin da tayi.

Maryam ta taba auren jarumi kuma mawaki Adam A Zango wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa, bayan Adam A Zango ya sake ta tayi wani auren wanda bai dade ba suka rabu.

Daga baya ta hadu da wani mutum suka cigaba da soyayya har da alkawarin zasu yi aure, wannan tasa ya basu aron gida suka zauna a Abuja ita da mahaiflyar ta, amma kafin a kai ga shirya maganar sai kawai aka ji tayi wannan sabon auren ba zato ba tsammani.

Majiyar ta fada wa wakilin mu cewa, Maryam zata tare ne a Maiduguri jihar Borno, inda can ne angon nata ya aje uwargidan sa da ‘yayan sa.

Rahoto daga👉 Fim Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button