Labaran Hausa

Ba ruwana da kamfen din Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, cewar jaruma Rahama Sadau

Ba ruwana da kamfen din Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, cewar jaruma Rahama Sadau

Jarumar masana’antar kannywood da Nollywood “RahamaSadau” ta nesanta kan ta da wani jerin sunaye da jaridar Punch ta buga mai nuna cewa tana daya daga cikin mata ‘yan fim da dan takarar zama shugaban kasa a jam’iyyar APC “Asiwaju Bola Ahmed Tinubu” ya nada a matsayin matanda zasu taya shi kamfen.

Rahama ta karyata labarin ne a soshiyal midiya a wani sako da tayi da Turanci inda ta ce: Thisis a fat big lieeeee. I am not a ware of this. I don’t know how my name made it to this list. Not in any way associated with this.

Ma’ana: Wannan babbar karya ce ni bani da masaniyar wannan ban san yadda aka yi sunana ya shiga wannan jerin ba, babu abin da yahada ni da wannan abin.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa, ba a san jarumar da shiga harkar siyasa ba sannan da alama ba’a tuntube ta ba kafin a fitar da sunayen, wanda hakan ne ya sa tayi wannan rubutu cikin bacin rai da mamaki.

Ban da ita Rahama, wasu mata ‘yan Kannywood dake cikin jerin sun hada da Saratu Gidado wato Daso, Kyauta Dillaliya, Samira Ahmad, Fati
Nijar, Mansurah Isah, Teema Makamashi, Ummi Gombe, Hadiza Kabara, Fati Karishma, Samira Saje da Hajiyan Nas.

Sai dai kuma tsohuwar jaruma Mansurah Isah tayi wa Rahama magana ta ce mata, kuskure ne da aka saka sunan Rahama a jerin.

A cewar Mansurah: Zuwa ga Rahama da bama sunan ki bane wanda ki ka gani sunan Rahama MK ne amma da yake ke kadai ce Rahamar dasu ka sani a Kannywood, sai suka dauka ke ce amma kada ki damu ba ke ba ce.

Mansurah wadda tayi dumu-dumu a harkar siyasar Tinubu ta nuna cewa, sune suka ba da sunayen da aka gani kuma basu ba da sunan Rahama Sadau ba sabida sun san ita ba ta harkar siyasa.

A cewar ta, ‘yan Kudu ne suka buga sunayen shi yasa suka yi kuskure domin basu san Rahama MK ta cikin diramar Kwana Casa’in ba.

Rahama Sadau dai ba tace wa Mansurah ko maiba amma ita Rahama MK sai murna take yi, domin har ta kwafe sunayen ta wallafa a shafinta tare da godiya.

Rahoto daga👉 Fim Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button