Advertisement
Labaran Hausa

Babu Abunda Yafi Dacewa Da Murja Kunya Kamar Aikin Lauyanci

Babu Abunda Yafi Dacewa Da Murja Kunya Kamar Aikin Lauyanci

A Jiyane Muka Kawo Muku Labarin Kada Keyar Da Kotu Tayiwa Yar TikTok Dinnan Mai Suna Murja Ibrahim Kunya Kan Cin Zarafin Da Tayiwa Jaruma Aisha Najamu Da Mai Wushirya

Tun Da Fari Dai Jami’an Yan Sanda Ne Suka Kama Ta Tana Daf Da Yin Dinnar Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarta A Yayin Da Suke Tare Da Mai Wushirya A Wani Hotel Kamar Yadda Mai Wushirya Ya Bayyanawa Duniya A Wani Faifan Bidiyo Da Ya Saki

Saide Bayan Tattaunawar Da Yan Sanda Sukayi Da Ita Tare Da Zayyano Mata Tuhumar Da Ake Mata Na Maganganu Batsa Tare Da Zage Zage A Kafar TikTok Ne Sai Murja Ta Basu Amsa Da Cewar Ita Maganar Zage Zage Ta Daina Insha Allah Sannan Kuma Maganar Batsa Kawai Tana Hawa Wakar Ado Gwanja Ne Kasancewar Mafi Akasarin Yan TikTok Na Arewa Na Amfani Da Wakar Ado Din

Inda A Lokacin Nan Sai Akaga Alamun Murja Kamar Ta Daina Wannan Dayen Aikin Na Zage Zage Wadda A Sanadiyyar Haka Wani Mai Kaunarta Ya Bata Shawarar Akan Ta Koma Makaranta Ta Karanchi Aiki Lauyanci Saboda Iya Maganarta Da Sarrafa Harshe

Saboda Kowane Dan Adam Akwai Baiwar Da Allah Yake Masa Saide Kuma Ba Kowane Ke Iya Gano Hakan Ba , Saboda Wani Za’a Haife Shi Da Baiwar Tasa Yana Aiki Da Baiwar Amma Baisan Yana Da Baiwar Ba

To Ita De Murja Tabbas Duk Wadda Ya Santa Ya Santa Ne Kan Magana A Kafar Tiktok Domin Inda Ta Fara Magana Kace Kanya Ce Take Zubowa Daga Kan Bishiya Ko Kuma Tamkar Zubar Ruwan Sama

Sannan Kuma Wannan Bawan Allah Ya Bawa Murja Shawarar Ne Ta Koma Makaranta Ta Karanchi Aikin Lauyanci Saboda Tana Da Mutane Sannan An Santa A Ko Ina Indan Ta Zama Lauya Zata Samu Shahara Saboda Mutane Zasuyi Ta Bata Aiki A Kotu Domin Ta Karesu Kan Wata Matsalar

Haka Zalika Wanda Ya Bawa Murjan Shawars Ya Samu Karfin Gwiwa Ne A Cikin Tattaunawar Da Akayi Da Ita Da Yan Sanda A Lokacin Da Aka Kamata Inda Take Cewa Bata Ma Kammala Karatun Sakandare Ba Ta Watsar Da Karatun

To Akan Wannan Maganar Ne Yasa Wanda Ya Bata Shawarar Ya Bata Shawarar Ta Koma Makaranta Sannan Inda Zata Koma Makaranta Tayi Waec Sannan Ta Nemi Babbar Makaranta Inda Zatayi Karatun Lauya Domin Babu Abunda Da Yafi Dacewa Da Ita Kamar Aikin Lauyanci

Amma Har Yanzu De Ba’aji Abunda Murja Ta Gaya Ba Kan Wannan Maganar ,Sai Kwatsam Akaji Cewar Kotu Ta Aika Da Ita Gidan Gyaran Hali Har Zuwa 16 Ga Wata February Domin Samun Cikakkun Hojoji Kan Shariar Tasu Na Aisha Najamu Da Mai Wushirya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button