
Babu wani abin farin ciki a duniyar nan fiye da Mace ta kasance a dakin Mijin ta, cewar matar jarumi Adam A Zango
Babu wani abin farin ciki a duniyar nan fiye da Mace ta kasance a dakin Mijin ta, cewar matar jarumi Adam A Zango
Safiya Chalawa, matar jarumin finafinan masana’antar Kannywood “Adam A Zango” ta bayyana ra’ayinta dangane da kasancewar mace matar aure a shafinta na Instagram.
A wallafar da tayi ranar Asabar ta bayyana cewa, abu ne mai matukar sanya mace murna ta kasance a cikin dakin mijinta kuma hakan yana kawo nutsuwa mara misaltuwa.
Safiya Chalawa ita ce matar jarumin tabiyar wacce a yanzu haka ta haifa masa kyakkyawar yarinya mai suna “Diana”.
An dade ana rade-radi yayin da wasu ke zargin cewa, yadda suka rabu da sauran matansa haka itama baza ta dade ba, amma kuma sai ga shi sun bamara da kunya.
Don yanzu haka zaune suke lafiyya kuma idan mutum yana bibiyar shafin jarumin da na matarsa, zai kula da yadda suke yawan yabon juna.
Tana yawan yabonsa tare da kiransa miji na gari mai halayen da bako wanne namiji ne yake da shi ba, kamar yadda ta fadi a ranar zagayowar haihuwar sa.
Shi ma yana yawan yabonta tare da cewa diyarsa zata yi alfahari nan gaba idan ta ganta a matsayin mahaifiyarta.
A wannan sabuwar wallafa da tayi cewa tayi: Yar uwata musulma mai aure, a duniyar nan babu abinda yafi kasancewarki mamatar aure dadi, ki kasance mai yawan yi wa Ubangiji godiya da ya azurta ki da miji na kwarai, ki kuma dinga nuna farinciki akan kokarinsa mijinki.
Ki yi masa godiya akan taya ki cika addininki da yayi, bayan aurenki da yayi.
Ta cigaba da shawartar mata akan yadda zasu tafiyar da rayuwar auren su ta hanyar kyautata wa mazajensu.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa