
Baiwar Tsayi Da Allah Yayiwa Wani Saurayi Ya Haifar Da Kece Kuce A Kafar Sadarwa
Baiwar Tsayi Da Allah Yayiwa Wani Saurayi Ya Haifar Da Kece Kuce A Kafar Sadarwa
Wani dan Najeriyar da Allah ya azurta shi da tsayi sosai ya haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta kamar yadda koda mutum na da tsayi idan ya tsaya kusa da shi sai ya gajarce.
An yi wannan cece-kucen ne a shafin Twitter bayan @alameengimba ya wallafa hotunansa tare da bakin da suka halarci bikin da ya halarta
Inda ya rubuta”Bakon bikin aure … Ina son daukar hotuna da gajerun mutane.”
@alameengimba na da tsayin da ya kai sahu shida da inci takwas.
Saide koda da ya wallafa wannan maganar ya samu tsokaci al’umma inda
@sopzeeworld tace “Mahaifiyata ta taba fada min cewa cin wake na iya sa mutum ya kara tsayi. Wa ya san buhun wake nawa wannan mutumin ya ci.
@earhmerd ya ce: “Tambayata a nan ita ce idan kana son sumbatar abokiyar zamanka a tsaye, yaya abin zai kasance?”
@ sadiqshettima89 ya yi tsokaci: “Shin kana da tsayi ne sosai ko kuma mutanen da ke kusa da kai ne gajeru? Ina taya kanwata tambaya ne.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.