Advertisement
Labaran Hausa

Ban Damu NanShiga Jahannama Ba: Mai Kudin Duniya Ya Bayyana Cewar Ya Kusa Mutuwar

Ban Damu NanShiga Jahannama Ba: Mai Kudin Duniya Ya Bayyana Cewar Ya Kusa Mutuwar

Mai kudin duniya, Elon Musk, ya yi wani rubutu a shafinsa na Twitter wanda ya girgiza mabiyansa a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, yana mai cewa ya kusa mutuwa.

Koda dai bai bayar da cikakken bayani kan halin da yasa shi fadin haka ba, mai kudin ya nuna rayuwarsa na gab da zuwa karshe.

Ya rubuta

Idan na mutu a cikin yanayi mai ban mamaki, ina alfahari da sanin ki/ka.”

Da yake martani, wani mabiyinsa mai suna @Almisehal wanda ya nuna damuwa game da rayuwar biloniyan ya ce ba zai mutu ba kafin lokacinsa.

Cikin haka sai ya kuma tambayi Musk kan ko har yanzu bai gane cewa akwai mahallicin duniyan nan ba, sannan ya bukaci da ya bayyana hakan idan har ya gano hakan kafin fitar ransa.

Da yake mayar masa da martani, Elon Musk ya fada masa cewa shi bai damu ba don an saka shi a wutar jahannama.

Ga yadda hirar tasu ta kaya:

@Almisehal:

“Ba za ka mutu ba kafin ranar ka Elon.

“Duk da haka, kai ka kasance mutum ne na musamman a wannan duniyar.

“Abu daya nake mamaki: A matsayinka na haziki, ba ka gano cewa akwai babban mahaliccin wannan duniyar ba tukuna?

“Idan ka yi, ka tabbata ka furta wannan kafin bugun zuciyarka ta karshe.

Allah ya albarkace ka.”

@elonmusk:

“Na gode da sa albarkar, amma ban damu da shiga jahannama ba, idan har wannan ne makoma na, tun da yawancin mutanen da aka haifa za su kasance a wurin.”

Ga Wallafawar Nan

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button