
Bani da burin kowa ya sanni a Duniya, cewar Sadiq Saleh mawakin Abin ya Motsa
Bani da burin kowa ya sanni a Duniya, cewar Sadiq Saleh mawakin Abin ya Motsa
Sadiq Saleh, sabon mawaki wanda ya samu shahara bayan sakin wakarsa mai taken “Abin ya motsa”, ya bayyana burinsa a rayuwa inda yace yana son ko ina a duniya a san shi kuma yanzu haka ya fara taka matakin.
A tattaunar da BBC Hausa tayi da mawakin mai karancin shekaru ya bayyana tarihinsa inda yace, an haife shi a Maiduguri kuma a nan ya taso sannan yayi karatunsa a can.
Yace ya kwashe shekaru yana yin waka kasancewar tun yana karami yake da burin zama mawaki, daga nan kuma ya hadu da abokai masu irin ra’ayinsa.
A cewar sa, ya yi wakoki na siyasa da na aure daban-daban kuma bai samu shahara ba sai a wannan sabuwar wakar da yayi ta Abin ya motsa, wacce kowa ya san shi da ita.
Yayin da aka tambaye shi wakar da yafiso a duk wakokin sa yace yafi son wakar Abin ya motsa, sai dai ba ita bace wakar da yafi shan wahala yayin rera ta ba.
Yace, wakar aure ta farko da yayi ne yafi wahala yayin yin ta,ya shaida cewa ba ya da wanı buri da ya zarce kowa na duniya ya san shi, kuma yanzu haka da alamu ya fara taka wannan mataki.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa
Ga cikekkiyar shirar tasu nan a kasa domin ku kalla ku saurara.