Advertisement
Labaran Hausa

Batun iskancin da Safara’u take yi a yanzu Rahama Sadau ta dora laifin a kan ‘yan kannywood

Batun iskancin da Safara'u take yi a yanzu Rahama Sadau ta dora laifin a kan 'yan kannywood

Kamar yadda kuka sani dai Safiyya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u korarriya ce a cikin shirin kwana casa’in mai dogon zango, wanda a yanzu ta koma mawakiya tare da maigidanta Mr 442.

Dalilin korar Safara’u daga cikin shirin kwana casa’in shine, bullar wata bidiyon tsiraicin ta a kwanakin baya wanda hakan ya janyo cece-kuce da maganganu daban-daban.

Ita ma Rahama Sadau ficacciyar jaruma ce a masana’antar kannywood wacce a kwanakin baya aka koreta daga masana’antar, bayan bullar wasu hotunan ta wanda ta dalilin su aka sani wani kafiri yayi batanci ga fiyayyan halitta Annabi Muhammad S.A.W.

To a yau dai “Northflixng” sun tattauna da Rahama Sadau akan fim din “Dan Iya”, da kuma rayuwar jarumi a kannywood.

Wanda a cikin tattaunawar tasu ne ta fadi wasu abubuwa da suke nuna cewa a dalilin ‘yan kannywood ne Safara’u ta tsinci kan ta a cikin wannan yanayin da take a yanzu.

Zaku iya kallon bidiyon da muka saka ta a kasa domin kuji cikekkiyar tattaunawar da aka yi da Rahama Sadau.

Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button