Advertisement
Labaran Hausa

Bayan Auren Lilin Baba Da Ummi Rahab, Lilin Baba Ya Raba Gari Da Yayan Ummi Rahab Yasir

Bayan Auren Lilin Baba Da Ummi Rahab, Lilin Baba Ya Raba Gari Da Yayan Ummi Rahab Yasir

Kamar Yadda Kuka Sani A Tsawan Watanni Shida Zuwa Bakwai Da Suka Gabata Ne Aka Daura Auren Jarumar Kannywood Ummi Rahab Da Mawaki Kuma Jarumi Lilin Baba Wadda Yasir M Ahmad Yayan Ummi Din Ne Suka Shiga Gaba Domin Yiwuwar Auren Bayan Jarumar Ta Raba Gari Da Mai Gida Adam A Zango

Adam A Zango Ya Kasance Shine Bakandamiyyar Haskarka Lilin Baba Tun Wakar Su Da Tayi Yawo A Arewa Da Ma Fadin Kasar Nan Baki Daya Wato Wakar ‘Lilin Baba’ , Haka Ma Itama Jaruma Ummi Rahab Adam A Zango Ne Ya Zama Sillar Haskakarta A Masana’antar Kannywood Tun Bayan Dawowarta Masana’antar Da Ta Fara Fito A Shirinsa Mai Suna ‘Farin Wata’.

A Yayin Da Aka Samu Dadaito Tsakanin Jarumin Barkwanchin Madagwal Da Yasir M Ahmad Ne Sai Wata Magana Ta Bullo Inda Suka Bayyana Cewar Anyi Amfanin Da Su Ne Domin Cimma Wani Buri Inda Daga Baya Akayi Watsi Dasu Kuma Suka Gane Suka Dadaita Tsakaninsu

Saide Yasir Ya Bayyana Cewar Bayan Anyi Amfani Dashi Wajen Cimma Burin Samun Auren Ummi Rahab Sau Daya Kawai Lilin Baba Ya Bashir Sukayi Waya Da Ummi Din Wadda Itama Ba Kai Tsaye Aka Kirashi Ba Wadda Koda A Shafinka Na Sada Zumuntarta Anyi Unfollowing Dinsa Wadda Bashi Da Tabbachin Ita Tayi Wannan Abu Kana Ko Kiran Lilin Baba Yayi Baya Amsa Kiransa Daga Baya Yaga Ba Amfanin Zama A Inda Ba’asan Ganinsa Sai Yayi Unfollowing Lilin Baban Kawai Ya Janye Daga Al’amarinsa

Yasir ya cigaba da cewa Bai san laifin da yayiwa Lilin baban ba ya dauki wannan mataki a kan sa ko dan ya cimma burin sa ne ya gama amfani da shi wajen samun abin da ya ke nema na auren Ummi yanzu yaga bashi da amfani Shiyasa ya biyo masa ta wannan harkar yake masa kora Da Hali

Saide A Bangaren Tattaunawar Da Tashar Tsakar Gida Sukayi Da Lilin Baba Ya Bayyana Cewar Shi Babu Sabanin Da Suka Samu Da Yasir Din, Game Da Kuma Korafin Da Yasir Din Yayi Na Kin Waya Da Kuma Unfollowing Dinsa Da Akayi A Shafin Ummi Din Babu Hannun Lilin Baba Cikin Wannan Abu, Abu Ne Dake Tsakaninsa Da Ummi Din Domin Wani Sabanin Suka Samu A Tsakaninsu Tun Lokacin Hidimar Bikinta ,Kuma Tun A Lokacin Yaso Yi Musu Sulhu Amma Ummin Din Bata Bada Hadin Kaiba

A cewar lilin Baba in da wani abu a tsakanin sa da yasir ai bazai kira shi a waya video call ya hada shi da ummin ba wanda sai da ya tsawatarwa Ummi din kafin ta yaddatayi maganada yasir din saboda tana fushi kuma ba yau suka fara samun sabani suna shiryawa ba meyasa wannan karon zai dora laifin a kansa saboda yana auren ta ai bashi da damar tilastata Mu’amala da wanda vata so musamman kasancewar ta matar aure

A karshe lilin baba ya bayyana shi baya son shiga irin wayannan kananun maganganun kowa ya sanshi ba mai yawan shiga kananan maganganu bane balle abin da ya shafi iyalin sa yana zaune Lafiya da Ummi tana masa biyayya fiye da yadda yai zaton zai samu daga gare ta dan haka baabin da zai ce mata Saide Allah ya saka mata da gidan Aljanna bai ga dalilin tilastata abin da bata so ba da bai zama wajibi ba tunda tana da hankalin ta tana kuma da damar yanke hukunchi rayuwarta da fatan Allah ya basu zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button