
Bayan Jiran Akwatin Gawar Sarauniyar Ingila Elizabeth Sojan Dake Gadin Akwatin Ya Rasu
Bayan Jiran Akwatin Gawar Sarauniyar Ingila Elizabeth Sojan Dake Gadin Akwatin Ya Rasu
Trooper Jack Burnell-Williams, matashi dan shekara 18 wanda ya yi gadin gawar Sarauniya Elizabeth ta II a wurin jana’izarta ya rasu.
A cewar The Telegraph, an gano gawar matashin ne a Barikin Hyde Park a Knightsbridge, Landan a ranar Laraba 28 ga watan Satumba.
Mahaifiyarsa, daga Bridgend, South Wales, ta yi alhinin rashinsa ta hanyar wallafa hotonsa a soshiyal midiya sanye da unifom dinsa.
Ta rubuta:
“Ban taba tunanin zan fada haka ba amma mu a matsayin iyali muna alhinin rashin dan mu.
Kafin rasuwarsa, iyalansa sun wallafa bidiyon dogarin a wurin bikin jana’izar sarauniya, tana cewa ‘muna alfahari’ da Mr Burnell-Williams saboda ‘yi wa sarauniya rakiya zuwa gidanta na gaskiya.’ Za a saki balan-balan don karrama shi a wannan makon
Kakakin Metropolitan Police ya ce:
“An kira yan sanda misalin karfe 3:48 a ranar Laraba 28 ga watan Satumba cewa an tsinci wani mutum baya numfashi a Barikin Hyde Park.
“Jami’an mu tare da motar kai daukin gaggawa suka tafi. An tabbatar da wani mutum dan shekara 18 ya rasu. An sanar da yan uwansa.
Kakakin yan sanda ya ce:
“Muna bakin cikin tabbatar da rasuwar Trooper Jack Burnell-Williams a ranar 28 ga watan Satumba a Hyde Park Barracks. Muna mika ta’aziyya ga iyalan sojan da abokansa a wannan lokacin.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.