
Bayan kwashe shekaru 47 da tafiya cirani da wani magidanci yayi yanzu ya dawo gida tsofai-tsofai ‘yayan sa sun kasa gane shi
Bayan kwashe shekaru 47 da tafiya cirani da wani magidanci yayi yanzu ya dawo gida tsofai-tsofai 'yayan sa sun kasa gane shi
Bidiyon wani magidanci da ya dawo daga cirani a kasar waje bayan kwashe shekara 47 ya ba masu amfani da yanar gizo mamaki matuka, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
A cikin bidiyon magidancin wanda ya tsufa ya tuna da gida inda ya dawo bisa mamakin ‘yan uwan sa daya ‘yayan sa.
Labarin magidancin mai suna “Peter Shitanda” tashar YouTube ta Afrimax English, ta wallafa shi.
Bidiyon ya sanya mutane da dama tofa albarkacin bakin su, a rahoton Jaridar Legit.ng.
Peter dan kasar Kenya ne ya bar kauyen su inda ya koma kasar Tanzania da fatan samun ingantacciyar rayuwa.
Da farko ya fara zama a birnin Nairobi kafin ya koma kasar Tanzania, inda yayi aiki a kusa da tsaunin Kilimanjaro.
Bayan ya kasa samun tagomashin daya fita nema Peter ya kuma kasa dawowa gida.
Iyalan sa sun yi zaman jiran sa cikin takaici yayin da matansa suka auri wasu mazajen.
Daya daga cikin ‘yayan sa namiji wanda yake da shekara hudu a duniya lokacin da ya tafi ya bar su, ya kasa gane mahaifin na sa lokacin da ya dawo tsotai-tsofai da shi.
Abin ban mamakin shine, magidancin bai dawo da wani abin arziki ba sai kawai wasu ‘yan jakunkuna duk kuwa shekarun da ya kwashe a wajen ciranin.
Ga cikekkiyar bidiyon a kasa domin ku kalla.