
Bayan kwashe tsawon watanni 5 tana kwana a kasa yanzu ta wallafa hoton wani katafaren gadon data saya take kwana a kai
Bayan kwashe tsawon watanni 5 tana kwana a kasa yanzu ta wallafa hoton wani katafaren gadon data saya take kwana a kai
Wata mata ta bayyana wa duniya hoton gadon data siya a shafinta naTwitter, @LeratoRSA, inda tace ta wahala a shekarar nan ta sha wahala mai yawa, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
Ta bayyana yadda ta kwashe tsawon watanni biyar tana bacci a kasa kafin Ubangiji ya azurta ta da kudi ta siya gado mai kyau.
Nan da nan mutane suka dinga yi mata fatan alkhairi ta hanyar tura mata sakwanni suna taya ta murna, kamar yadda ta bayyana a shafinta.
Inda ta fara da cewa: Na wahala kwarai a wannan shekarar, amma na samu haske a wannan gabar, ‘yan Najeriya da dama sun dinga cewa gadaje masu kyau ba su da arha a zamanin nan.
Muna taya ta murna ganin cewa ta wahala da farko amma yanzu ta samu sauyi mai kyau.
Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakin su karkashin wallafar da tayi, ga kadan daga cikin su.
Current2620 yace: Lale la wannan ai babbar nasara ce kiji dadin ki komai kankantar nasarar ka ya kamata kayi murna a kanta, kiyi bacci mai kyau ‘yar uwa.
Cleeeyo- yace: Gaskiya babbar nasara ce a gare ni in samu aiki har in siyawa kaina gado.
Chifchiduku yace: Ya kamata ayi murna akan nasara komai kankantarta.
Ngiyakubongela cc tace: Wannan ya sa min kwarin gwiwa nagode.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa