
Bayan watanni biyu da auren su, Angon ya bankawa kansa wuta sabida Amaryar tana gallaza masa
Bayan watanni biyu da auren su, Angon ya bankawa kansa wuta sabida Amaryar tana gallaza masa
Bayan watanni biyu da wani dan shekara 30 yayi aure, matarsa tana yawan zagi da kushe shi.
Afolabi mazaunin yankin Iree ne dake jihar Osun an samu nasarar ceto shi bayan ya banka wa kansa wuta, kamar yadda “Labarun Hausa” ta ruwaito.
An tattaro bayanai akan yadda mutane suka kai masa dauki bayan jin ya fara rusa kuka, ya bayyana cewa ya yi aure ne a watan Yulin 2022 kuma matarsa tana yawan azabtar da shi, hakan ne ya tunzura shi ya yanke shawarar halaka kansa.
Afolabi ya yi bayanin ne a gadon asibiti inda yace bakar azabar da amaryar tasa ke gallaza masa ne ya sa ya dauki matakin.
Kamar yadda ya bayyana cewa: Na yanke shawarar kawo karshen komai ne a ranar juma’a shi yasa naje har gidan mai na sayo man fetur, na nufi dajin kusa da makarantar Baptist dake Iree inda na bankawa kaina wuta.
Nayi tunanin azabar da nake aha ne yasa na yanke shawarar halaka kaina, bakin talauci da azabar da matata ke min yasa na dauki wannan matakin, na aure ta ne a watan Yulin wannan shekarar.
Jama’a ne su ka ji ni ina ihu yayin kona jikina shi ne su ka yi gaggawar ceto ni su ka kai ni asibiti.
Matar Afolabi mai suna “Ifedolapo” tace, bata san dalilin da yasa zai halaka kansa ba, amma tana zaton sabida har yanzu bata samu juna biyu bane ya yanke shawarar halaka kansa.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa