
Bayan ya auri Makauniya shekaru kadan da suka wuce shima ya makance
Bayan ya auri Makauniya shekaru kadan da suka wuce shima ya makance
‘Yan uwan wani mutum suna ta zundensa bayan ya fada tarkon soyayyar wata mata mai cutar makanta, kamar yadda “Labarun Hausa” suka wallafa.
Mutumin wanda asali daga Arusha yake cikin kasar Tanzania, yana tsaka da neman halaliyarsa sai ya hadu da wata makauniya wacce yaji kaf duniya babu wacce tayi masa sai ita.
Mutumin mai suna Rashidi Apahamanyi Musasigye ya bayyana kudirinsa na auren Lilian.
Wannan lamarin ya bai wa Lilian mamaki inda taga mutumin da ba yada wata nakasa ya bukaci ya zabe ta a matsayin matarsa, kamar yadda Afrimax English ta bayyana.
Anan ne Lilian ta bayyana wa Rashidi labarin yadda mijinta ya bar ta bayan sun haifi yara biyu ba tare da sake waiwayarta ba.
Hakan bai sa Rashidi ya sauya niyyarsa ba, amma dai yace mata yana son rayuwa da ita har karshen rayuwarssa.
‘Yan uwansa sun nuna masa cewa, bai dace ya aureta ba zai fi kyau idan har ya auri wacce zata iya tallafa masa maimakon mai nakasa.
Duk da haka, sun yanke shawarar yin aurensu inda suka cigaba da rayuwa cikin soyayya da kauna.
Sai dai bayan shekaru kadan aka kusa halaka Rashidi ba tare da yayi komai ba, wanda daga bisani kuma aka tura shi kurkuku.
Bayan wani lokaci kadan ya makance, Rashidi ya zargi ‘yan uwansa da yi masa mugun aikin, inda yace ba su da niyyar ganin ya cigaba.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa