Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Bidiyan Bikin Wata Budurwa Data Bayyana Naira 15 Miliyan Suka Kashe Ya Dauki Hankula

Bidiyan Bikin Wata Budurwa Data Bayyana Naira 15 Miliyan Suka Kashe Ya Dauki Hankula

Wata matashiya yar Najeriya, Jessica Ayodele, ta je shafin soshiyal midiya a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba don bayyana makudan kudaden da ta kashe a kan aurenta.

Matar ta bayyana cewa daga ita har mijinta sun kashe zunzurutun kudi har naira miliyan 15 a kan kasaitaccen bikin aurensu

Jessica ta bayyana cewa a lokacin da suke shirye-shiryen aurensu a watan Afrilu, duk tunaninta ba za su kashe kudi fiye da naira miliyan 5 ba wajen gayyatar mutane 100 kacal.

Jessica ta bayyana cewa karbar dakin taro a Lagas na da matukar tsada domin yana farawa daga N800,000 kan baki 200 zuwa naira miliyan 4.1 na baki 1000.

Ta kara da cewar sun kashe miliyan N1.2 da N650,000 kan shirya wajen shagalin biki kawai.

An kashe naira miliyan 1.1 wajen daukar hotuna da bidiyoyinsu.

Lamukan kwalba sun ja naira miliyan 1.6, yawon amarci ya ja naira miliyan 2.5. Jessica ta shawarci mutane da su yi daidai ruwa daidai tsaki.

Kalli Wallafawar Anan

Masu sauraranmu a koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button