Advertisement
Labaran Hausa

Bidiyan Mai Kama Da Shugaban Kasa Muhammad Buhari Da Ya Dauki Hankula

Bidiyan Mai Kama Da Shugaban Kasa Muhammad Buhari Da Ya Dauki Hankula

Mai tsananin kama da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janyo cece-kuce bayan ya tsinkayi wani gidan mai cike da salo irin na shugaban kasan.

A bidiyon TikTok din da ke tashe, matashin wanda yayi shiga tsaf irin ta shugaba Buhari ya Juya kan jamaa yayin da ya ke tate hannayensa na lakwashe ta bayansa.

Gajeren bidiyon ya samu sama da masu kallo 440,000 a yayin da ake rubuta wannan rahoto.

Duban da aka yi wa asusun TikTok din mai suna @buhariangus ya nuna cewa an sadaukar da dukkan bidiyoyin da aka wallafa ne don mai kama da Buhari kuma ya na da mabiya 13,000.

Wani zai iya sakankancewa matashin yayi amfani da wannan shuhurar inda ya zama mawallafi da bidiyoyin mai kama da Buhari.

Kalla bidiyon a kasa:

Tsokaci Al’umma

Mosuro Azeez Olanrewaju tace:

Kai anya da gaske ku ke yi?”

Dodo Ox07 yace:

Asalin Buharin ba ya iya kai hannunsa baya kamar yadda wannan yayi.”

MuhammadMtm yace:

“Matukar ka taba yin soja, toh har abada kai soja ne. Yadda ya tsaya kamar yana filin fareti.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button