
Bidiyan Malamin Makaranta Da Yaje Banki Karbar Alabashin Da Jaka ‘Ghana Must-Go’ Ya Dauki Hankula
Bidiyan Malamin Makaranta Da Yaje Banki Karbar Alabashin Da Jaka 'Ghana Must-Go' Ya Dauki Hankula
Yan soshiyal midiya sun yi martani ga bidiyon wani mutumin da aka gani a banki dauke da jakar ‘Ghana Must Go’ rataye a kafadarsa.
A cewar @nanahook00, wacce ta yada bidiyon a TikTok, mutumin malamin makaranta ne, kuma ya zo da jakar ne domin karbar albashinsa na wata takwas da yake bin gwamnati .
A cikin bidiyon mai tsawon dakiku 10, an ga lokacin da malamin ke muzurai a cikin bankin, ya kuma nuna kamar ba komai yayin da yake harkar dake gabansa.
Kyautablog bata iya tantance gaskiyar cewa da gaske malamin makaranta ne kuma ya zo karbar albashinsa ne ba. An dai bayyana cewa, lamarin ya faru ne a kasar Ghana.
Kalli Bidiyan Anan
Tsokacin Al’umma Game Da Wannan Bidiyan
Toto yace: “Watakila ya zo ne daga Qnet a tunani na.”
$FAZ$ yace: “Na tabbata bankin sun rufe bayan ya cire kudinsa.”
Abena Adoma yace: “Wannan sabon shigan malamin makaranta ne.”
masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.