Advertisement
Labaran Hausa

Bidiyan Matashin Da Ya Kera Mota Da Tarkace Sannan Ya Tukata A Unguwarsu Ya Dauki Hankula

Bidiyan Matashin Da Ya Kera Mota Da Tarkace Sannan Ya Tukata A Unguwarsu Ya Dauki Hankula

Wani dan Najeriya ya bar jama’ar baki bude a shafukan sada zumunta lokacin da aka ga kalar motar da ya kera wata da tarkacen karfe mara amfani.

A cikin wani faifan bidiyo da aka yada a Instagram ranar 15 ga Disamba, @onlynuelpls ya nuna lokacin da matashin ke tuka motar akan titin garinsu.

A faifan bidiyon, an ga motar da matashin ya kera a tsaye babu kofa balle wani rufi, kawaia bude take kowa ya sha iska.

Yan Najeriya da dama sun ce ya burge su kuma sun yaba masa bisa irin fikira da yake da iya, sun yi martani da yawa mai daukar hankali.

View this post on Instagram

A post shared by OnlyNUELpls (@onlynuelpls)

@clearcut lawncare ya ce

“Dan uwa ya sanya jirgin ruwan da ba a iya gani yana motsi.”

@onosedvgbd ya ce:

“Tdan da ace manyan mutanenmu za su saka hannun jari a irin wannan tsagwaran basira.

@tylereick 97 ya ce:

“Dan uwa kana tuka kwarangwal kawai.”

@logan olm ya ce:

“Mutumin ya sami sabuwa Lamborghini, Allah ida nufi”

@jasonsntony13 ya ce:

“Wannan abin ban mamaki ne, babu tsaro amma abin ban mamaki ne. Kasancewar yana da wannan fikiri, ya kenan idan yana da wadata.

@ilove my_ninja ya ce

“Ku sama wa wannan mutumin aikil ldan ya kera wannan to ya cancanci aiki inda zai yi amfani da wannan ilimin!”

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button