
Bidiyan Wani Yaro Bakanike Yan Turanchi Ya Bawa Mutane Mamaki
Bidiyan Wani Yaro Bakanike Yan Turanchi Ya Bawa Mutane Mamaki
Dandazon mutane a shafin TikTok sun kamu da kaunar wani yaro mai suna Mubarak saboda irin kwazon da yake dashi.
Hakan ya fara ne daga wani bidiyon da @ayofeliberato ya yada na lokacin da Mubarak ke karanta wata muhawara da ta dauki hankali ya yadu a intanet.
Kwarewarsa a yaren turanci ta ba jama’a mamaki, wannan yasa suka ce ya yi matukar burge su.
Mubarak, wanda yaro ne a shagon masu sana’ar kanikanci yana muhara ne kan yin karatu da rana a madadin dare.
Ya kawo hujjojinsa masu daukar hankali, inda ya ce dare mahutar bawa ce, don haka babu batun karatu da dare, sai dai da rana.
Kalli bidiyan anan
Saide Koda da mutane suka ga wannan bidiyan sun shiga takaichi Mai yasa baya karatu kasancewar baiwar Iya turanchin da Allah Yayi masa tare da Yi masa fatan Nasara
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.