Advertisement
Labaran Hausa

Bidiyan Yadda Amarya Ta Gigita Ango Yayin Da Take Kirjinsa A Wajen Biki Ya Sumbatu Yasa Shi Bata Makudan Kudi

Bidiyan Yadda Amarya Ta Gigita Ango Yayin Da Take Kirjinsa A Wajen Biki Ya Sumbatu Yasa Shi Bata Makudan Kudi

Wani bidiyon da @oppyjay alaga ya yada ya nuna lokacin da amarya ta gamu da ango cikin farin ciki a wurin biki, ango ya jika ta da kudaden kasar waje.

A lokacin wani taron gargajiya, amaryar ta durkusa a gaban angonta dauke da jaka yayin da MC ke rera waka.

A bidiyon da aka yada, an ga lokacin da ta matso, ta kama kirjin ango tana shafawa, hakan ya ba shi annashuwa.

Yayin da take shafa shi, angon ya fasa ba ta kudi kadan da ya yi niyya tun farko, sai kawai ya cusa hannu a aljihu ya kwaso kudaden kasar waje masu yawa ya saka a jakarta.

Kalli Bidiyan Anan

 

Martanin jama’a

Ga kadan daga abin da jama’a ke cewa game da wannan lamari da ya dauki hankalin ‘yan soshial midiya.

Awoyemi Balikees:

“Wannan amaryar ba ta wasa ko kadan”

Celine dion:

Mai daukar hoto na shirya fashi a gaba.”

0Z X

“Kar dai Dala da Fam din Burtaniya nake gani? Anti, meye kika saka ajikinki.”

Adeline 0023:

“Mai daukar hoto mamaki yake wani tsafin wannan matar ta yi amfani dashi.”

Akleh skin:

“Wannan shine ake kira ATM na gaske.. wow”

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button