Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Bidiyan Yadda Ango Ya Dauki Amarya Akan Babur Ya Dauki Hankula

Bidiyan Yadda Ango Ya Dauki Amarya Akan Babur Ya Dauki Hankula

Wani ango ya dauko amaryar sa akan babur domin zuwa wajen daurin auren su.

Mutane da dama Sun tofa albarkacin bakin su akan bidiyon.

A wani bidiyon da wani mai amfani da@Mujunimedardmujuni ya saka a TikTok, angon cikim kasaita ya dare kan babur din tare da amaryar sa da kuma babbar kawar amarya. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Alamu sun nuna cewa angon da amaryar sa suna kan hanyar su ta zuwa wurin daurin auren su ne.

Amaryar tayi ado cikin kayan amare yayin da ango shima ya sha kwalliya Cikin kayan angwanci.

Sai dai ba a sani ba ko mutumin dan achaba ne ko kuma da shi da amaryar sa sun yanke shawarar kawai su hau babur ne a ranar daurin auren su.

Kalli Bidiyan Anan

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun Kalli wannan bidiyan zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button