
Bidiyan Yadda Wani Bako A Wajen Biki Ya Gwangwaje Amarya Da Ango Da Kyautar A Wajen Bikin Su
Bidiyan Yadda Wani Bako A Wajen Biki Ya Gwangwaje Amarya Da Ango Da Kyautar A Wajen Bikin Su
Akwai wani lokaci da aka samu rudani daga bisani dariya ta barke a wajen liyafar wani biki, bayan wani mutum ya gabatar da wata kyautar da ba a saba bada ta ga ma’aurata ba.
A wani bidiyo da yayi yawo a dandalin TikTok, mutumin ya isa inda ma’auratan suke, inda ya gabatar musu da kyautar lcce.
Ma’auratan sun dara yayin da mutumin ya bukaci daukar hotuna dasu tare da iccen.
Bidiyon ya yadu a kafafan sada zumuntar zamani inda wasu suka siffanta kyautar mutumin a matsayin abu na rashin kyautawa. Wasu kuma sun kwashi nishadi tare da yin sokaci mai ban dariya.
Kalli Bidiyan Anan
Saide Koda Da Mutane Suka Ga Wannan Bidiyan Sun Fara Tofa Albarkacin Bakinsu
user495679630804 ya ce:
“Meye maanar wannan iccen, a kowacce al’ada hakan na nufin wahała, tsanani da rashin sa a. Ba ma wani iccen ba fatan alheri bane.”
dic ky ya ce:
“Ni kam nayi imani da cewa daga zuciyarsa kyautar take. Taya murna shine babban abua rayuwa.”
winniewins 1 ta ce:
“Babu abun da ba zai iya faruwa ba a wannan duniyar”
ogelism 111 ya ce:
“Meye ido na bazai gani ba.”
simon ya ce
“Al’ada ita ce abu mafi karfi dake nuna ko waye mutum ina son hakan! kada kayi hukunci da kallon iccen. Waye zai iya fada min ma’anar iccen.”
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun Kalli wannan bidiyan zamu so karben a sahen mu na tsokaci.