Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Bidiyan Yadda Wata Baturiya Tazo Kasar Nijeriya Domin Sayan Turmi Da Tabarya Ta Koma Ya Dauki Hankulan Sosai

Bidiyan Yadda Wata Baturiya Tazo Kasar Nijeriya Domin Sayan Turmi Da Tabarya Ta Koma Ya Dauki Hankulan Sosai

Wani bidiyon da wata kyakkyawar mata farar fata na yadda ta siya turmi da tabarya a lokacin da ta ziyarci Najeriya ya ba da mamaki.

A bidiyon da ta yada, matar mai suna Joana ta bayyana cewa tana kaunar cin tuwon doya irin na ‘yan Najeriya.

Matar ta ce ta siya turmi da tabaryar ne a Legas domin take iya daka doya domin cin tuwo irin na ‘yan Najeriya.

Ta kuma koka da cewa, ta sha siyan tuwo daga gidajen cin abinci na ‘yan Afrika mazauna turai, amma ta ce sam babu dadi, kamar ruwa.

Bayan da Joana ta yada bidiyon, jama’a da dama ‘yan Najeriya sun yi ca a shashen martani, inda suka bayyana yabo a gareta.

Mutane da yawa sun kira ta matar kirki, sun kuma nuna suna matukar kaunarta.

Kalli bidiyon

@FemiGrand yace: “Na fada miki haka tun kafin ki bata hanya zuwa Albaniya….Ke asalin ‘yan Najeriya ba wai a alaka ba, daga asalin tushe. Mun san matanmu.

oyekanmiabiodunol yace: “Kai kai kai! Wannan abu ne ya yi kyau. Allah ya yi albarka! Kin hadu gaskiya

user6036935716151 yace: “Yanzu na san daga rayuwarki ta baya ke ‘yan asalin Afrika ce, kuma ‘yar Najeriya.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun Kalli wannan bidiyan zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button