
Bidiyan Yaro Mai Birkilanchi Yana Kuka Ya Koma Makaranta Ya Dauki Hankula
Bidiyan Yaro Mai Birkilanchi Yana Kuka Ya Koma Makaranta Ya Dauki Hankula
Kamorudeen, karamin yaron nan wanda bidiyon sa yana aikin birkilanci yana kuka, ya karade yanar gizo ya koma makaranta.
Wannan labarin mai dadin saurare dai wani mai suna Lukman Samsudeen ya sanya shi a manhajar TikTok. Jaridar legit ta rahoto.
Labarin Kamorudeen ya bazu ne bayan bayyanar bidiyon sa yana kuka yana aikin birkilanci.
Bidiyon ya sosa zukatan mutane sosai inda aka rika tambayoyin ko ina iyayen sa suke da kuma meyasa yake aikin karfi yana dan karamin yaro da shi.
Nan da nan sai ta bayyana cewa mahaifin sa ya rasu sannan yana ganin mahaifiyar sa ne sau daya kawai a shekara a cikin watan Disamba.
A cikin sabon bidiyon da Lukman ya sanya a TikTok, yaron yayi kyau sosai cikin kayan makarantar sa da kuma sauran sabbin kayan sanyawa da aka siya masa
Tsokacin Al’umma Game Da Bidiyan
user36783072399emmson ya rubuta: Allah ya albarkaci duk wanda yake da hannu wurin taimakawa yaron nan ya samu rayuwar mai kyau.
Kalli Bidiyan Anan
Emaska rubuta: Wow na ga wannan yaron yau a wata wallafa.
manuel Jnr ya rubuta: Ka kyauta sosai dan’uwa
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun Kalli wannan bidiyan zamu so karben a sahen mu na tsokaci.