
Bikin auren jarumar kannywood Rukayya Dawayya da da shugaban hukumar tace fina-finai Afakalla ya matso kusa
Bikin auren jarumar kannywood Rukayya Dawayya da da shugaban hukumar tace fina-finai Afakalla ya matso kusa
A yanzu da damina ta fara zuwa karshe hankalin wasu ‘yan fim ya koma kan batun auren nan da aka jima ana tsimayen sa, wato na jarumar Kannywood “Hajiya Rukayya Umar Santa” wacce aka fi sanin ta da Rukayya Dawayya da Shugaban Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Alhaji lsma’il Na’abba Afakallah.
Wasu da mujallar Fim ta zanta da su, amma suka bukaci a sakaya sunan su, sun ce sun kosa azo a yi bikin suna fadin a gaskiya sun dace.
Mujallar Fim taji daga wata majiya mai karfi kan lamarin cewa, shirye-shiryen bikin sun kankama.
A kan gaskiyar batun auren majiyar tace: To ai ba tun yanzu aka fara yin batun auren ba, ko makaho a Kannuwood ya san akwai soyayya tsakanin Rukayya Dawayya da Afakallah.
Soyayya ce da aka dade ana yin ta a karkashin kasa ba tare da sun bayyana wa duniya ta sani ba, sai a yanzu da aski yazo gaban goshi ne yasa ita Rukayya Dawayya ta fara dora hoton Afakallah a “status” din ta na WhatsApp da daTikTok.
Da kuma Instagram tare da yin wasu bayanai masu nuna alamar akwai soyayya maikarfin gaske a tsakanin su.
Majiyar ta kara da cewa: Akwai maganar auren kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci za’a iya yin sa.
Ana cewa, ba wani taro za’a yi ba za’a dai daura aure ne kawai amarya ta tare, amma dai mu mun dage a kan lallai sai an yi dina.
Rukayya Dawayya ba karamar jaruma ba ce kuma shi oga kowa dai ya san matsayin sa da mukamin sa a gwamnati da ma siyasa.
Don haka za muyi biki sosai, da zarar sun kammala shirin da suke yi za’a ji sanarwar daurin auren ba wani abu bane da zamu boye.
Wakilin mu ya lura da yadda jarumar wadda kuma furodusa ce ta mayar da al’amuran ta nasoshiyal midiya ga Afakallah, musamman wajen wallafa hotunan sa da bidiyon sa, har ma da na ‘yayan sa a shafukan ta.
Shi din ma ya na kulata a duk lokacin da ta wallafa abin da ya shafe shi.
A sakon da ta wallafa a instagram a ranar 15 ga Yuli 2022 Rukayya Dawayya tace, samun Afakallah da tayi a matsayin miji, Allah ne ya amsa addu’ar ta.
Tace, samin masoyi na gaskiya a wannan zamanin da rashin gaskiya yayi yawa sai karfin addu’a.
Alhamdu lillahi ya Rabbi lakalhamdu wash shukhur. Allah na gode maka daka amsa addu’a ta. Khairun nas man yanfa’un nas.
Hoton sa data dora a ranar 14 ga watan Agusta tare da alamomin kauna da kuma addu’ar “Khairunnas man yanfa’un nas” ya kara bayyanar da soyayyar tasu a fili.
Dimbin ‘yan fim da sauran jama’a sun taya Rukayya Dawayya da Afakallah murnar wannan abu da suke shirin yi, suna fadin Allah ya kai mu lokacin lafiya.
Rahoto daga👉 Fim Magazine