Advertisement
Labaran Hausa

Bikin Sallah: Yadda Daso ta raba wa mata 60 kyautar atamfofi

Bikin Sallah: Yadda Daso ta raba wa mata 60 kyautar atamfofi

Jaruma a a Kannywood, Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso), ta yi wani namijin ƙoƙari domin tallafa wa mata masu ƙaramin ƙarfi guda 60 inda ta gwangwaje su da turamen atamfa domin su samu abin da za su saka domin yin kwalliyar Sallah.

Ta yi rabon atamfofin a safiyar ranar Asabar, 15 ga  Afrilu, 2023 a wajen taro mai suna Daso Event Centre.

Gidan taron, wanda mallakin ta ne, ya na ‘Yanƙusa, ya na kallon baifas kusa da NNPC a Kano.

Tun da farko da ta ke bayani kan manufar rabon atamfofin, Hajiya Saratu ta ce, “Manufar shirya wannan taron dai shi ne domin mu haɗu da ku mu yi zumunci da kuma ganin juna, kamar yadda ku ke samun labari na ko ku ke gani na a talbijin, domin ni a gaskiya ban taɓa ganin ku ba sai a yanzu da mu ka haɗu, don ba ni na gayyato ku ba, na sa a gayyato mini mata masu buƙatar taimako daga cikin marayu, zawarawa da kuma ‘yan mata. Don haka ba ni da wata sanayya a tsakani na da ku sai yanzu da mu ka haɗu a wannan wajen.

“Saboda haka mu na fatan za mu yi amfani da wannan dama wajen kyautata alaƙa tare da yi wa juna addu’a.”

Ta ƙara da cewa, “Ganin halin da mutane su ke ciki a wannan lokacin, na yi amfani da ɗan kuɗin da na ke samu a kamfani na na Daso Entertainment na samar da atamfa ta mutane guda sittin don su samu kayan da za su saka a bikin Sallah. Kuma mu na fatan wannan niyyar tamu ta zama mai amfani a gare mu duniya da lahira.

“Don haka in godiya a gare ku da ku ka samu zuwa domin karɓar wannan kayan tallafi, kuma za mu ci gaba da yin hakan nan gaba kamar yadda mu ke da tsari na ciyarwa da kuma rabon kayayyakin abinci da mu ke yi a birni da ƙauyuka. Da fatan Allah ya mayar da kowa gidan sa lafiya.”

Matan da su ka samu atamfofin sun nuna farin cikin su tare da godiya, da kuma addu’a ga Daso kan manufar ta ta taimakon masu ƙaramin ƙarfi

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan kun karanata wannan bayanin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button