Advertisement
Labaran Hausa

Budurwa ta fusata ta bazama neman saurayin da zata yi wuff da shi ko ta halin kaka

Budurwa ta fusata ta bazama neman saurayin da zata yi wuff da shi ko ta halin kaka

Wata budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana cewa, ta gaji da zama ba saurayi, Budurwar ta garzaya wani babban shago domin nemo saurayi.

Bayan ta isa shagon, Budurwar tayi bidiyo inda take bayyana cewa ba taje shagon bane domin siyawa kanta kayayyaki ba.

A cewar ta, makasudin zuwanta shagon shine samo saurayi, ta kara da cewa bata damu ba da duk wanda ta samu ko da kuwa saurayin wata ne daban, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.

A kalaman ta tana cewa: Kuna dai ganin inda nake yanzu ko ban zo nan ba domin siyan wani abu nazo neman saurayi ne.

Zan shiga shagon nan da sunan ubanhiji, sannan ‘yar uwa ki sani cewa idan saurayin ki yazo wajena shikenan tafaru ta kare ya tafi kenan, da gaske ake hidimar ba’a bori da sanyin jiki ba’a tsaya wa sanya.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kan wannan bidiyon matar, ga kadan daga cikin su.

Iteomaonye ta rubuta cewa: Wane ‘yar uwa ta, mazajen arziki na can na aiki a ofisoshin su, Yan Yahoo-yahoo zaki hadu da su a nan.

Veevogee ya rubuta cewa: Wasu na rabuwa wasu na neman saurayi, kaga wannan rayuwar.

Vickyflamez ya rubuta cewa: Ki sani cewa cikin sauki zaki iya kwace makashin matar aure a shagon, mutane ya kamata su dinga taka tsan-tsan.

Ga bidiyon matar a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button