
Budurwar Yar Nijeriya Ta Tunkari Wani Saurayi A Cikin Banki Ta Karbi Lambar Wayarsa
Budurwar Yar Nijeriya Ta Tunkari Wani Saurayi A Cikin Banki Ta Karbi Lambar Wayarsa
Wata budurwa yar Najeriya da ke yin bidiyoyin barkwanci a TikTok ta je shafin intanet don nuna wani bidiyo wanda a ciki ta tsara wani matashi.
A cikin bidiyon, budurwar ta tunkari wani ma’aikacin banki inda ta bayyana masa cewa lallai shi din yana da kyau. Bayan sun sha hannu da shi, sai ta fada masa cewa tafin hannunsa na da matukar laushi.
Mutumin ya karbi wannan yabo da budurwar tayi masa hannu bibbiyu. Bayan ta bar mutumin, sai budurwar ta nuna dan takardar da mutumin ya rubuta masa lambarta a ciki.
Mutane da dama sun yi al’ajabin abun da zai faru idan har ya zamana mutumin na da aure. Yayin da wasu ke da tambayoyi da dama, wasu sun so yadda ta tunkari lamarin.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun Kalli wannan bidiyan zamu so karben a sahen mu na tsokaci